Rahotanni sun bayyana cewar jami’an tsaro sun kama ɗan wasan tsakiyar Manchester City, Matheus Nunes, kan zargin sa da satar waya.
A cewar Dailymail, an kama an tsare ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Portugal, inda ake masa tambayoyi kan zargin satar waya a gidan casu a birnin Madrid na ƙasar Spain.
An ruwaito cewar ɗan wasan am tsare sa a yankin La Riviera, a ranar 8 ga watan Satumba inda aka masa tambayoyi kan lamarin.
An ce an kama ɗan wasan, da misalin ƙarfe 5:30 na safe bayan an zarge shi da ɗaukar wani mutum mia shekara 58, da ya yi ƙoƙarin ɗaukarsa hoto a banɗakin gidan casun, ba tare da izininsa ba.
Ɗan wasan mai shekaru 26, an ce ya ɗauke wayar mutumin ne cikin fushi tare da ƙin dawo masa da ita.
An ruwaito cewar ’yan sanda sun kama shi tare da gano wayar a tare da shi.
Tsohon ɗan wasan na Wolves, ya sauya sheƙa zuwa Manchester City kan kuɗi Yuro miliyan 62.