Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tura da tallafin kayan abinci zuwa jihar Oyo, domin taimakon wadanda rikicin kalibanci ya ritsa dasu a baya-bayan nan.
Kwankwaso ya samu wakilcin Hon. Muktar Umar Yarima, wanda ya jagoranci gabatar da kayan abincin ga shugabannin Hausawa mazauna yankin kasuwar Sasa.
- Mata ta mari mijinta don ya ladabtar ta ’ya’yansu
- An gurfanar da matashi kan tayar da zaune tsaye
- Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya
“Mutanen da rikicin nan ya ritsa da su, suna cikin wani mawuyacin hali suna bukatar dauki daga jama’a, shi yasa jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aiko da kayan abinci da za a raba musu.
“Yana da kyau bayan Kwankwaso a ce akwai wadanda za su taimaka musu, ko ba komai mutum ya taimaki ‘yan uwansa da kuma addininsa,” cewar Yarima.
Yarima, wanda ke zaman tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, ya jagorancin tawagar wasu ‘yan Kwankwasiyya wajen kai tallafin.
A sakamakon rikicin kabilancin da ya barke tsakanin Hausawa mazauna garin Sasa da ke Jihar Oyo da Yarabawa, Hausawa mazauna garin, suna neman jama’a da su tallafa musu musamman da kayan abinci, biyo bayan asarar da suka tafka.
Daga cikin kayan abinci da Kwankwaso ya aike sun hada da shinkafa buhu 200, ruwan roba katan 200 da kuma lemon roba shi ma katan 200.
Tawagar da ta jagoranci lamarin ta gabatar da kayan tallafin abincin ga Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, don raba wa mutanen da rikicin ya shafa.
“Mutane da yawa sun yi kaura, wasu kuma sun fantsama wasu wuraren amma duk da haka za mu yi wakilici ta yadda tallafin zai je gare su.”
“Muna godiya ga Kwankwaso da irin wannan taimako da ya yi mana, wannan ya nuna cewa shi jagora ne na gari,” a cewar Maiyasin.
Aminiya ta ruwiato cewa rikicin kabilanci da ya barke a kasuwar Sasa da ke birnin Ibadan makonnin baya, ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyin mutane da dama wanda ba su ji ba su gani ba.
Bayan faruwar rikicin wasu Gwamnonin Arewa suka kai ziyara inda suka gana da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da zummar nemo mafita kan lamarin.
Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso, ya yi kaurin suna wajen shiga sha’anin ‘yan Arewa da ke zaune a wasu sassa na Najeriya.
Ana iya tuna cewa Kwankwaso lokacin da ya ke zaman gwamnan Kano, ya fanshi wasu ‘yan Arewa mazauna Jihar Legas da aka daure su a gidan Kaso a bisa kuskure.