Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da manyan na hannun damansa, Okezie Ikpeazu na Jihar Abin, Samuel Ortom na Binuwai da kuma Sheyi Makinde na Jihar Oyo sun tafi Turai.
Wata majiya mai tushe a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas ta ce a ranar Juma’a da dare suka tashi daga Fatakwal zuwa birnin Madrid na kasar Spain.
- Kiwon kaji: Yadda aka yi wa masu neman tallafi damfarar N819m a Kano
- Ghana ta koro ’yan Najeriya 16 kan damfara ta intanet
Majiyar ta ce ana sa ran Gwamnan Inugun zai same su a Spain, inda za su tattauna kan rikicin cikin gida na jam’iyyarsu ta PDP gabanin zaben 2023 da aka fara yakin neman zabe.
Wike da manyan abokan nasa su yi tafiyar ce a ranar da ya yi taron ’yan jarida, inda ya caccaki Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, yana mai cewa dole ya sauka daga mukaminsa.
A lokacin taron, Wike ya kuma yi barazana ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, da idan shi da magoya bayansa suka bar PDP, Atikun ba zai ci zaben 2023 ba.
Ya ce “Mun yanke shawarar ci gaba da zama a Jam’iyyar PDP, dalili kuwa shi ne idan muka ce za mu bar ta tare da magoya bayanmu ba za ta iya cin zabe ba.
“Amma fa, dole wannan mutumin ya sauka daga mukaminsa, a bai wa yankin da ya kamata ya fito da shugaban jam’iyyar.
“Su din me suka sallama, ko suna ganin idan gwamnoni biyar suka sauya sheka zuwa wata jam’iyya PDP za ta yi wani katabus?”
Atiku Abubakar dai ya dakatar da kaddamar da yankin neman zabensa da farko, inda ya yi ta bibiyar Wike domin shawo kansa.
Amma daga baya da yake magana kan tattaunawarsa da wakilan da Atiku ya tura na karshe suka tattauna, Wike ya nuna ya hakura, ya amince da Atiku, amma dole Ayu ya yi murabus.