✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin PDP: Kotu ta hana PDP hukunta Wike

Wike na ci gaba da yin takun saka da shugabancin jam'iyyar PDP na kasa.

Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya umarci Jam’iyyar PDP da kada ta dauki wani mataki da nufin dakatarwa ko korar Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike daga cikinta.

Alkalin ya bayar da umarnin ne kan karar da Wike ya shigar na shugabannin jam’iyyar.

Wadanda aka shigar karar sun hadar da Jam’iyyar PDP, kwamitin gudanarwarta na kasa, kwamitin zartarwa na kasa, shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu; sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Wike ya bukaci kotun da ta hana duk wani yunkuri da ya shafi barazanar dakatar da shi ko kuma korar shi daga jam’iyyar.

Bayan karanta takardar shaidar goyon bayan karar da wata Precious Ikpe ta gabatar, kotun ta amince da bukatar gwamnan kan hana dakatar da shi.

Wike dai ya shiga takun saka da shugabancin jam’iyyar PDP da kuma ɗan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, tun bayan da ya sha kaye a hannun Atikun a zaben fid-da-gwanin jam’iyyar.

Gwamnan da sauran takwarorinsa biyar wadanda ake kira da G-5, sun kaurace wa shiga yakin neman zaben jam’iyyar.

A baya-bayan nan Wike ya hana Atiku filin gudanar da yakin zabe a Jihar Ribas.

Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba zai bayyana matsayinsa kan dan takarar da shi da mutanensa za su mara wa baya a zaben da za a gudanar nan da mako biyu.