Gwamnatin Pakistan sun kama wani babban jigo na jam’iyyar tsohon Firayim Minista Imran Khan a ranar Alhamis, a yayin da gwamnati ta tura sojoji don murkushe tarzomar da ta barke sakamakon kama Khan kwanaki uku da suka gabata.
A cikin dare ne dai jami’an tsaron suka kama Shah Mahmood Qureshi, wanda ya kasance Ministan Harkokin Waje na shekara hudu a lokacin da Imran Khan ke firayim minista.
- Yadda aka kama miyagun kwayoyi miliyan 8.2 a Saudiyya
- Yadda likita ya yi wa mara lafiya fyade a asibiti
An kuma kama wasu manyan jiga-jigai biyu na jam’iyyar PTI ta Mista Khan — Asad Umar da Fawad Chaudhry a ranar Laraba.
Kawo yanzu an kashe akalla mutum biyar bayan da tarzomar da ta biyo bayan kama Mista Khan da hukumar yaki da rashawa ta kasar ta yi a ranar Talata ta kara munana.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Pakistan ke a kasar mai mutane miliyan 220 ke fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki da kuma jinkirin samun dauki daga Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) tun watan Nuwamba.
Masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin gine-ginen sojoji tare da kai farmaki gidan wani babban hafsan soji a birnin Lahore da ke gabashin kasar; sun kuma kai hari tare da kona wasu gine-gine da kadarorin gwamnati.
A ranar Laraba gwamnatin kasar ta amince da bukatar gwamnatin birnin Islamadan da kuma biyu daga cikin larduna hudu na kasar — Punjab da Khyber Pakhtunkhwa, wadanda kowacce daga cikinsu tungar Khan ce, — na tura sojoji domin dawo da zaman lafiya.
Rundunar ’yan sandan Islamabad ta fada a safiyar ranar Alhamis cewa sojoji sun isa babban birnin kasar.
’Yan sanda dai sun kama masu zanga-zanga sama da 1,300 a lardin Khan na Punjab saboda tashin hankali.