✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Gaza: Ƙasar Falasɗinawa mai cikakken ’yanci ce mafitar —Najeriya

Najeriya ta yi kira a aiwatar da tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra'ila masu cin gashin kansu don tabbatar da zaman lafiya a…

Gwamnatin Najeriya ta bukaci Isra’ila ta bari a shiga da kayan agaji ga miliyoyin Falasɗinawa da hare-harenta a ya raba da muhallansu.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce rikicin ya jefa fararen hula da ba su da hannu a kansa cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga Isra’ila ta bari a shiga da kayan agajin jinkai Zirin Gaza.

Ministan ta wata sanarwa a ranar Asabar ya jaddada kira da a aiwatar da tsarin kasashe biyu na Falasdinawa da na Isra’ila masu cin gashin kansu don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Ya bayyana cewa “Najeriya na kara kira da a gaggauta tsagaita wuta a koma kan teburin sulhu don samun mafita ta lumana, sannan a aiwatar da tsarin kasashe biyu masu cin gashin kansu don warware rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa”.

Kiran na zuwa ne mako uku bayan Isra’ila ta ƙaddamar da hari a yankunan Falasɗinawa a Zirin Gaza inda ta kashe mutum akalla 7,000, akasarinsu kananan yara da mata, daga ranar 7 ga Oktoba.

Mako guda kuma ke nan da aka fara shigar da kayan agaji ta kasar Masar, sakamakon hana shiga da fita da Isra’ila ta yi a Gaza.

Isra’ila ta yanke ruwan sha da wutar lantarki da man fetur a Gaza, lamarin da ya sa asibitocin da ke Gaza suka tsaya, haka ma ayyukan jin kai a akasarin yankin.

Kasashen duniya da dama sun yi tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza, inda ta raba kimanin Falasɗinawa miliyan daya da muhallansu.

Tun a makon jiya kayan masarufi a shagunan da ke Gaza, yankin da Isra’ila ta kai harin jirage a asibitoci da makarantu da wuraren ibada da gidaje.

Ana zargin Isra’ila da manyan laifukan yaki ciki har da amfani da bamabamai masu ɗauke da haramtattun sinadarai a kan mata da ƙananan yara da sauran fararen hula a Zirin Gaza.

Isra’ila ta ƙaddamar da kashe-kashen ne da sunan ramuwar gayya kan harin da kungiyar Hamas ta kai mata a ranar 7 ga wata, inda mayakan kungiyar suka kashe mutum 1,400, suka yi garkuwa da wasu 200.