Da alama, rikicin cikin gidan da ke addabar jam’iyyar adawa ta PDP ya kara kazancewa bayan da bakwai daga cikin shugabanninta na kasa suka ajiye mukaminsu.
Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) ne ya tabbatar da ajiye aikin nasu ranar Talata.
- DSS ta kama matasa 5 da suka yi garkuwa da mai shekara 6 a Kano
- Za a fara korar masu fallasa takardun sirrin gwamnati daga aiki
Sai dai bai yi cikakken bayani a kan lamarin ba.
Shugaban PDP na kasa dai, Uche Secondus wanda wa’adinsa zai kare a watan Disamba mai zuwa na fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mukaminsa.
Ko a kwanan nan sai da Shugaban ya shiga car baki da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike wanda ya rika sukarsa a bainar jama’a.
Amma Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi yunkurin sasanta su ko da yake hakansa bai kai ga cimma ruwa ba.
Jam’iyyar PDP dai a cikin watanni uku ta yi fama da matsalar sauya sheka musamman daga wasu daga cikin gwamnoninta.
Gwamnonin sun hada da David Umahi na Ebonyi da Ben Ayade na Kuros Riba kuma Bello Matawalle na Zamfara wadanda suka koma APC.
Hakan dai ya sa mambobin jam’iyyar da dama sun yanke kauna daga shugabancin na Secondus.
A watan Yulin da ya gabata ma, wani dan Majalisar Wakilai daga jam’iyyar, Rimamnde Shawulu, ya bukaci Secondus din ya ajiye mukaminsa saboda gaza magance yawan barin jam’iyyar da ake yi.
Sai dai yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan a kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.