✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Benuwai da Taraba: Ci gaba da shirin wargaza Arewa ne

Tambayar da masana tarihi da masu sharhi ke tsoron amsawa ita ce, wai tsohon shugaban kasar  Najeriya Dokta Nnamdi Azikwe, wanda ake yi wa lakabi…

Tambayar da masana tarihi da masu sharhi ke tsoron amsawa ita ce, wai tsohon shugaban kasar  Najeriya Dokta Nnamdi Azikwe, wanda ake yi wa lakabi da “ZIK” na da hannu a juyin mulkin 15 ga Janairun 1966? To koma ba shi da hannu yana da masaniyar cewa za a gudanar da wannan juyin mulki. Muna ganin idan har kasar Birtaniya wadda ta yi wa Nijeriya mulkin mallaka za ta kyankyasa wa Firayiminista Minista Tafawa Balewa cewa akwai shirin za a yi musu juyin mulki, kuma idan har Firimiyan Yammacin Nijeriya Samuel Ladoke Akintola zai samu labarin juyin mulkin, kuma har ya taho Kaduna wajen Sardauna domin su gudu, to babu wani dalilin da za a ce Zik duk da ba ya kasar ba shida masaniyar juyin mulkin.

Yana da kyau mu fahimci wani abu kadan daga rayuwar Zik. Na farko yana daya daga cikin manyan ‘yan gwargwarmayar da suka yaki Turawan mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Wannan ko shakka babu.Ga shi ya samu damar zuwa kasar Amurka, inda har ya samu shaidar digirin digir-digir, baiwar da takwarorinsa irin su Awolowo da Sardauna ba su samu ba. Bayan dawowarsa daga Amurka, ya zauna kasar Ghana, inda ya fara wallafa jaridarsa, inda ya yi amfani da wannan dama ya yi ta caccakar Turawan mulkin mallaka.Ya dawo Legas ya ci gaba da wallafa jaridarsa, wadda ta mayar da hankali kacokan wajen yakar mulkin mallaka da sarakunan da ake ganin suna goyon bayan tsarin. Watakila a Najeriya, idan mutum ya cire Herbert Marcaulay wanda aka fi sani da uban kwatar ‘yanci, wato “Father of Natitonalism” to babu wanda ya kai Zik. Masana tarihi sun bayyana Zik a matsayin kwararren mai jawabi. A lokacin duk wani taro da za a yi na ‘yan boko, to in ba Zik, wannan taro bai kai taro ba.

To sai dai kamar sauran mutane, duk irin baiwar da Allah ya yi wa Zik, da kuma kirarin da ake mai na dan kishin kasa, ba dan kishin kabila ba, sai ga shi ya taka muhimmiyar rawa wajen ruguza kungiyar matasan Nijeriya wadda aka fi sani da turanci da “Nigerian Youth Mobement” Masana tarihi irin su marigayi Dokta Yusufu Bala Usman sun bayyana wannan kungiya, a matsayin gangariyar kungiyar  gwagwarmaya ta gaskiya da ta taka muhimmiyar rawa wajen kwato wa Najeriya ‘yanci. A wani littafi da marigayi Cif Obafemi Awolowo ya rubuta, ya bayyana yadda Zik ya fice daga kungiyar, sannan ya koma yana sukar jajirtattun mutanen da ke fafutikar samar wa Najeriya ‘yanci a wancan lokaci.Ya dinga amfani da jaridarsa, yana sukar Yarabawa abin da Awolowo ke ganin alamar siyasar kabilanci ta shigo a siyasar Najeriya. Kada mu manta dama kuma NYM ita ce ta kawo karshen siyasar jam’iyyar NNDP ta Herbert Marcaulay. Saboda haka Zik ya je ya jona da Herbert Marcaulay a sabuwar jam’iyyar da ya kafa ta NCNC, wadda daga baya, bayan mutuwar Marcaulay, ya zama shugaban ta. Awolowo ya bayyana Zik a matsayin mutumen da ke da wani kudirin na mulkin kasar, wanda yai ta amfani da jaridarsa yana kambama kansa, har mabiyansa, musamman Inyamurai na kiransa da “Zik of Africa” wato Zik na Afirika ya wuce ma Najeriya.

To sai dai kash, duk da Zik ya zama shugaban kasa, amma na jeka-na-yi-ka abin da bai mai dadi ba, domin ainahin iko yana hannun Firayiminista, dan Arewa. 

Bayan da aka gudanar da zaben 1964, Zik ya yi mursisi, ya ki ya kira Tafawa Balewa domin a kafa gwamnati. A cewar Zik ba shi da kwarin gwiwar yin haka, domin wai zaben na cike da magudi. Wannan kiki-kaka ta jefa kasar cikin rashin tabbas wanda sai da kyar, aka shawo kan al’amarin bayan manya da ke ciki da wajen kasar nan, sun saka baki.

Wannan na nuni da cewa ko da rantsar da Firayiminista Balewa ba da son ran Zik ba, don haka tafiyar dole ce kawai za a yi.

Hujjoji da suka bayyana daga baya kamar yadda wani mashahurin dan jarida a Kano mai suna Prince Ajayi Memaiyetan ya  bayyana a wata makalarsa, ya nuna Zik ya zama jakadan kasar Biyafara. Wannan dan jarida wanda a wancan lokaci yana aiki da jaridar New Nigeria, kuma shi ne wanda aka tura wurin yakin Biyafara ya zauna a Nsukka da Ore kafin kuma a tura shi Nairobin kasar Kenya inda yake aiko da rahotanni,  cewa Zik ya je kasar Tanzaniya domin neman kasar da ta amince da kasar Biyafara. Kada mu manta Tanzaniya ita ce kasar Afirika ta farko da ta amince da kasar Biyafara.

Kazalika, taken kasar Biyafara waka ce da shi Zik ya rubuta ta dan kanshi, ita wannan waka, ita ce ta zama taken kasar Biyafara.Ko wadannan hujjoji da muka kawo yanzu da kuma rubutuna na baya, shin  sun isa a ce Zik na da hannu a juyin mulkin 15 ga Janairun 1966 ko kuma da goyon bayan sa, kai me karatu ne kawai za kai ma kanka alkalanci.

Juyin mulkin 15 Janairu,1966, juyin mulki ne da manyan sojojin kabilar Ibo suka kitsa shi kuma suka aiwatar. Bayan sun yi abinsu, sun kafa hujjoji cewa wai sun yi ne saboda matsalar cin hanci da rashawa, kabilanci musamman a harkar daukar sojoji da yi musu karin girma da sauran su. Tun wancan lokaci duk juyin mulkin da soja sukai, sai sun kafa irin wadannan hujjoji ciki har da wanda su Dimka suka yi wa ma Murtala, to amma a kodayaushe, cin hanci da kabilanci ya fi muni karkashin mulkin soja.

Maganar ko Hassan Usman Katsina na da hannu, wannan ma, wasu makaryata ne masu son sake rubuta tarihi ke nuna Janar Hassan na da hannu ciki. Dalilin su na kokarin goga ma Hassan kashin kaji, bai wuce yunkurin a nuna juyin mulkin ba wai na wata kabila guda ba ne. Masana tarihi sun nuna ko lokacin da  madugun juyin mulkin a Kaduna, Manjo Chukuma Nzeogwu Kaduna, ya tambayi Hassan ko yana tare da su, inda Hassan  ya ce da shi “E”, bakin alkalami ya riga ya bushe, domin a lokacinma sun riga sun kashe duk wanda suka tsara za su kashe, don haka amsawar Hassan kawai ya yi tane domin ya tsira da kanshi. Kuma koda masu nuna cewa ai Hassan ya amfana daga juyin mulkin ta hanyar ba shi mukamin gwamna, to idan muka dubi abin da ya biyo baya, da rawar da Hassan ya taka lokacin yakin basasa da irin tattaunawa daban-daban da aka yi za mu fahimci sam Hassan bai cikin masu goyon bayan su. Sabanin Ojuku wanda daga karshe shi ya jagoranci yakin basasa daga bangaren ‘yan tawaye.

Duk da cewa ranar 15 ga watan Janairu ce aka kashe shugabannin kasar nan na farko, wadanda suka yi fafutukar korar Turawan mulkin mallaka, sai dai kash wai maimakon a tuna da su, sai aka koma tuna mutanen da su ne suka kashe su, suka bata duk wani shiri da kasarmu ta fara, tare da kawo mulkin soja, suka jefa kasar cikin yakin basasa. Ta yaya za a ce ranar da sojoji suka kashe su Tafawa balewa, Sardauna, Akintola,da sauran manyan sojojin farko kamar Zakari Maimalari ita ce za a maida ranar bikin tunawa da tsofaffin sojoji? Shin wannan ba kokarin halatta mummunan ta’asar da aka aikata ba ne a daren 15 Janairu,1966?

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina

Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa 08165270879.