Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa rikicin da ke faruwa tsakanin Azerbaijan da Armenia ka iya rikida zuwa wani yaki na yanki.
“Dole ne mu kula sosai wajen tabbatar da yakin da ke faruwa tsakanin Armenia da Azerbaijan bai rikida ya koma wani tashin hankali na yanki ba.
“Zaman lafiya shi ne kashin bayan aikinmu kuma muna fatar wanzar da zaman lafiya a yankin cikin lumana,” kamar yadda Mista Rouhani ya fada ta kafar talabijin.
Ya kuma ce Iran ba za ta lamunta ba da “kasashen duniya su girke ’yan ta’adda a kan iyakokinta ta hanyar fakewa da duk wani abu”.
A nashi bangaren, Shugaban Kasar Azerbaijan, Ilham Aliyev ya ce kasarsa za ta koma zama teburin sulhu da Armenia bayan kawo karshen mummunan matakan sojin da ke faruwa a rikicin na yankin Nagorno-Karabakh, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha, TASS ya ruwaito shi yana cewa.
Shugaba Aliyev, wanda ya yi magana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin ta wayar tarho, ya fada yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Rasha cewa Turkiyya tana da damar shiga tsakanin warware rikicin.