Fadar Shugaban Kasa ta shiga tsakani a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a Jihar Kano, ta hanyar kiran taron gaggawa tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Wata Majiya da ke kusancu da Gwamnan ta bayyana mana cewa Gwamnatin Tarayya musamman ta taso jirgi daga Abuja zuwa Kano ranar Juma’a domin kawo karshen rikicin jam’iyar da ya ki ci ya ki cinyewa.
- Malami ya fasa takarar Gwamnan Kebbi, zai ci gaba da rike mukamin Minista
- Taliban ta wajabta wa mata sanya nikabi a Afghanistan
Taron dai kamar yadda majiyar ta bayyana an kira shi ne domin dakatar da yunkurin Sanata Shekarau ne ficewa daga APC don komawa NNPP da ke kara mamaya a halin yanzu.
Jamiyar ta NNPP karkashin jagorancin madugun Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso dai na ci gaba da karbar jiga-jigan ’yan siyarsar Kano daga jam’iyyun APC da PDP, kuma tuni rahotanni ke bayyana shirye-shiryen karbar Sanatan a ranar Asabar.
Kazalika a maraicen ranar Juma’a ne aka hangi Gwamna Gandujen ya kai wa Sanatan ziyara gidansa da ke Mundubawa a Kano duk dai a kokarinsa na hana shi sauya shekar.