Rikicin ya barke a jam’iyyar PDP reshen jihar Legas bayan Kwamitin Gudanarwa ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar, Injiniya Adedeji Doherty bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun sanar da dakatarwar ne a ranar Juma’a bayan taron gaggawa na mambobinta suka yi tare da nada Mista Waliu Hassan, a mataimakin shugaban jam’iyyar na rikon kwarya.
Kwamitin dai ya amince da dakatar da Mista Gani Taofeeq da Mista Nurudeen Adewale daga jam’iyyar.
Sauran mambobin zartarwa na Jam’iyyar PDP na jihar a wurin taron tattaunawar sun hada da Cif Taiwo Kuye, Mataimakain shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da Kudu maso Yamma; Alhaji Segun Sowole, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na yankin Legas ta Tsakiya da Mista Tejumade Muyideen, mai ba jam’iyyar shawara a kan harkokin doka.
Mambobin sun zargi Doherty da yi wa PDP rikon sakainar kashi wajen tafiyar da al’amuran ta.
Sai dai Doherty ya mayar da martani ga kwamitin, inda ya ce Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ne kawai zai iya dakatar da shi daga mukaminsa.
Da yake magana a madadin jam’iyyar a lokacin taron da aka gudanar a sakatariyarta, Sakataren PDP a jihar, Muiz Shodipe, ya yi zargin cewa an karkatar da duk kudaden da aka samo kuma aka bayar da su don taimakon jama’a da kuma mambobin jam’iyyar.
Ya kara da cewa an kama Doherty da laifukan da suka hada da yi wa jam’iyyar zagon kasa tare da hada baki da wasu jam’iyyun wajen cin amanar ta da kuma kawo mata nakasu.
Bugu da kari, ya ce tun da Doherty ya zama shugaban jam’iyyar tsawon shekara daya, bai taba halartar tarukan da jam’iyyar ta ke gudanarwa ba ko sau daya.