Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya ce janye kalubalantar takarar Aisha Binani.
Nuhu Ribadu, wanda ya sha kaye a zaben fid-da-gwanin gwamna a jam’iyyar APC a hannun Sanata Aishatu Ahmed Binani, ya kalubalanci zaben, inda kotun tarayya ta zaben tare da bayyana cewa jam’iyyar ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023 a Jihar Adamawa.
- Qatar 2022: Maroko ta yi waje da Spain a bugun fanereti
- ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a Sakkwato
Kotun daukaka kara, ta mayar da Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaben, inda Ribadu ya ce zai garzaya kotun koli.
Sai dai Ribadu a wata takarda, ya ce zai hakura ya mara mata baya.
A cikin sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata, Ribadu, ya ce ya yanke shawarar yin watsi da bukatarsa ne domin ci gaban jam’iyyar.
Ribadu, ya sake nanata cewa ya yanke shawarar daukar wannan matsaya ne domin maslahar jam’iyyar, sannan ya bukaci dukkanin magoya bayansa da su goyi bayan Binani kan takararta ta gwamna.
“Na tuntubi iyalina da abokan siyasa da shugabannin jam’iyya a matakai daban-daban kan mataki na gaba. Bugu da kari, na yi tunani sosai kan masalahar da za a samu musamman burina na tsayawa takarar gwamnan Adamawa.
“Dalilin da ya sa nake son mulkar jihar shi ne don samun damar yi wa jihata hidima a matsayin gudunmawar da zan iya bayarwa.”
Ya ce tun da farko ya tunkari kotun ne saboda bai samu wani abin da ya dace a cikin koken nasa ba amma bayan kotun daukaka kara ta mayar wa Binani takara, ya ga bukatar hakura.
“Ba mu yarda da hukuncin ba amma ba ni da niyyar kara daukaka kara.”