Jami’an tsaro, wadanda suka hada da ’yan sanda da sojoji, sun kama masu zanga-zangar lumana ta #RevolutionNow akalla 60 a Abuja, babban birnin tarayya.
Masu zanga-zangar lumanar na bin titunan manyan biranen jihohin kasar nan ne domin tuna zagayowar shekara guda da gudanar da zanga-zangar lumana ta farko ta #RevolutionNow, wadda aka yi a ranar5 ga watan Agusta, 2019.
Wanda ya shirya gangamin, Omoyele Sowore, a shafinsa na Twitter ya ce jami’an tsaro sun ci zarafin masu zanga-zangar lumanar a Legas.
“’Yan sanda sun tsayar da masu zanga-zangar lumana ta #RevolutionNow a Gadar Third Mainland. Sun tauye musu hakkinsu na dan Adam ta hanyar tursasa musu zuwa ofishinsu”, inji shi.
Wani jagoran zanga-zangar Deji Adeyanju ne ya ce jami’an tsaro sun kama fiye da mutum 60 daga cikinsu a Abuja.
Ana gudanar da zanga-zangar ne dai a birane daban-daban na Najeriya.