✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta samu kyautar Naira Biliyan 1.2

Kulob din Real Madrid da ke Spain ya samu kyautar Yuro miliyan 3 (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 209) a ranar Lahadin da ta…

Kulob din Real Madrid da ke Spain ya samu kyautar Yuro miliyan 3 (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 209) a ranar Lahadin da ta gabata jim kadan bayan ya lashe Kofin Royal Super Cup a Saudiyya.

Kulob din ya samu wannan makudan kudi ne jim bayan ya lallasa kulob din Atletico Madrid da ci 4-1 a bugun finareti.

Wannan ne karo na 11 da kulob din ya lashe wannan kofi a tarihi.

Gasar wacce ta gudana a Saudiyya a karon farko, manyan kungiyoyi hudu da ke Spain ne suka fafata a tsakanin ranakun Alhamis zuwa Lahadi na makon jiya.

Kungiyoyin sun hada da na FC Barcelona da Balencia da Real Madrid da kuma na Atletico Madrid.

A wasan farko Real Madrid ce ta lallasa Balencia da ci 3-1 yayin da Atletico Madrid ta doke FC Barcelona da ci 3-2 inda aka yi wasan karshe a tsakanin kungiyar Real Madrid da Atletico Madrid.

Kulob din Atletico Madrid da ya kasance na biyu ya samu kyautar Yuro miliyan 2 (kimanin Naira miliyan 806).