✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar LaLiga

Madrid na saman teburin gasar LaLiga da maki 78 daga wasanni 31 da ta buga.

Kungiyar Kwallon Ƙafa ta Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar LaLiga bayan doke Real Mallorca da ci ɗaya mai ban haushi har gida.

Ɗan wasan tsakiyar Madrid, Aurien Tchouameni ne, ya jefa mata ƙwallo ɗaya tal a minti na 48 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Real Madrid ce ke jan ragamar teburin gasar da maki 78 daga wasanni 31 da ga buga.

Sai Barcelona a matsayin mataki na biyu na maki 70 daidai daga wasanni 31 da ta doka.

Kungiyar Girona tana mataki na uku da maki 65 daga wasanni 31 da ta, yayin da Athletico Madrid ke mataki na huɗu a gasar da maki 61 daga wasanni 31 da ta doka.

Yanzu haka dai sauran wasanni bakwai a kammala gasar LaLiga ta bana, inda daga ƙarshe za a gane ma ci tuwo.

Madrid dai za ta sake kece raini tsakanita da Manchester City a wasan zagaye na biyu na Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a ranar Talata a filin wasa na Etihad.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a gidan Madrid an kece raini, inda aka tashi 3 da 3.