✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid da Manchester United za su fafata a gasar cin kofin Amurka

kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da ke Sifen da na Liberpool da Manchester United da kuma na Manchester City da ke Ingila sun bayyana…

kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da ke Sifen da na Liberpool da Manchester United da kuma na Manchester City da ke Ingila sun bayyana kudurinsa na ziyartar Amurka don fafatawa a gasar cin kofin Champion da ke Amurka ta shirya.
Haka kuma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ta Inter Milan da Roma daga Italiya da kuma ta Olympiakos na daga cikin wadanda za su fafata a gasar.
Gasar za ta gudana a tsakanin rananun 27 ga Yuli zuwa 4 ga Agustan wannan shekara don tantance kungiyar kwallon kafar da za ta yi nasara.
Ana sa ran za a raba kungiyoyin takwas gida biyu ne don fafatawa da juna.  kungiyoyin da suka kasance na daya da na biyu daga kowane rukuni ne za su fafata a matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal  yayin da za a yi wasan karshe a ranar 4 ga watan Agustan wannan shekara a filin wasa na Miami Sun Life da ke Amurka.
Gasar za ta gudana ne a birane 11 da ke Amurka da suka hada da Charlotte da Chicago da Dallas da Denber da Minneapolis da New York da Philadelphia da Phonenid da Pittsburg da Washington DC da kuma birni daya da ba a ambaci sunansa ya zuwa wannan lokaci ba.
Kulob din Real Madrid ne ya lashe kofin a bara bayan ya buga wasan karshe a tsakaninsa da kulob din Chelsea na Ingila da ci 3-1.