Akwanakin baya mun duba kadan daga cikin irin la’anun da Allah Ya furta a kan mutum domin zunubin da ya yi lokacin da ya ke cikin gonar Adnin. Yanzu mutum ya iske kansa a waje; ba a cikin gonar ba kuma, inda ba shi da bukatar komai na kyautata rayuwa. Allah Ya shirya wa mutum cewa ba zai bukaci komai ba muddin yana cikin wannan gonar da shi Allah Ya dasa. Shirin Allah daga farko shine, mutum ya yi rayuwarsa a fuskar Allah, kullum cikin tsarki a wurin da ya rigaya ya shirya; yanzu mutum na fuskantarkalubalen rayuwa a wuri daban da inda Allah Ya nufa lokacin da Ya halicce shi. To, yaya irin wannan sabuwar rayuwa take?
Tsoro na farko ya shigo cikin mutum:
Lokacin da Allah Ya halicci mutum, Ya yi shi ne domin ya yi mulki bisa dukkan abin da Ya halitta. Ya kamata mutum ya yi wa Allah sujada; haka nan Allah zai ji dadin zumunci da mutum a kullum, zunubi ne ya kawo tsoro a cikin zuciyar mutum tun daga farko. “Sai suka ji muryar Ubangiji Allah Yana yawo a cikin gona da sanyin yamma: mutumin da matatasa suka buya daga fuskar Ubangiji Allah a cikin itatuwan gona. Ubangiji Allah kuma ya kira mutumin, Ya ce masa, Ina kake? Shi kuwa ya ce, na ji motsinka cikin gona, na ji tsoro, domin tsirara nake: na kuwa buya.” (Farawa 3 : 8 – 10). Zunubi shi kan kawo tsoro cikin zuciyar mutum, domin akwai hukuncin Allah a kan kowane irin zunubi, zunubi ne kan sa mutum ya yi kokarin buya daga fuskar Allah. Koda yake ba wanda ya isa ya boye wa Allah. Har wa yau, idan mun lura, duk lokacin da ka yi wani abin da bai cancanta ba a gaban Allah, ba ka samun kuzarin zuwa gabanSa musamman lokacin addu’a, domin Allah da muke bautawa ba Ya wasa da zunubi ko kadan; shi Mai tsarki ne.
Kisa na farko ya faru:
Da mutum ya iske kansa a waje, tunanin mugunta ne kadai ya cika masa zuciya, mu lura da halayen ’ya’yan Adamu daga wannan wuri “MUTUMIN kuma ya san Hawa’u matatasa; ita kuwa ta yi ciki, ta haifi Kayinu, ta ce, na samu namiji da taimakon Ubangiji. Kana ta haifi kanensa Habila. Habila kuwa makiyayin tumaki ne, amma Kayinu manomi ne. Ana nan ya zama Kayinu ya dauka daga cikin amfanin kasa ya kawo baiko ga Ubangiji. Habila kuma ya diba daga cikin ’ya’yan fari na garkensa; daga cikin masu kiba ya kawo su. Ubangiji Ya kula da Habila da baikonsa. Amma bai kula da Kayinu da baikonsa ba. Kayinu fa ya ji haushi kwarai, gabansa kuma ya fadi. Ubangiji kuma Ya ce ma Kayinu, don me ka ji haushi? Don me kuma gabanka ya fadi? Idan ka kyautata ba za a amsa ba? Idan kuwa ba ka kyauta ba, ga zunubi yana kwance a bakin kofa: a gareka kuma nufinsa ya koma, za ka shugabance shi kuma. Kayinu kuma ya fada wa dan uwansa Habila. Ana nan ya zama, lokacin da suna cikin saura, Kayinu ya ta sar wa Habila kanensa, ya kashe shi.” (Farawa 4:1-8).
A wannan lokaci, Adamu da matarsa Hawa’u sun soma samun ’ya’ya, yanzu akwai wa da kanensa wato Kayinu da Habila. Kayinu dai manomi ne Habila kuma mai kiwo ne, yana da tumaki. Duka su biyu suka yi tunanin kawo baiko ga Ubangiji Allah. Sai Ubangiji Allah Ya karbi baikon Habila na Kayinu kuma ya ki. Dalilin da ya sa Kayinu ya ji haushi ke nan, sai ya rudi dan uwansa suka shiga daji cikin saura, a wurin ya kashe Habila. Farkon kisa ken an cikin wannan duniya. Kuma zunubi ya kawo wannan irin halin. Kisa ba aikin Allah ba ne, Allah Mai bada rai ne Shi. Ina so mu lura, mene ne ya sa Allah Ya karbi baikon Habila kuma ya ki na Kayinu?
Kafin Ubangiji Ya karbi kowace irin hadaya daga wurin mutum; abu na farko da Yake dubawa ba yawa ko kankantar hadayar ba ne, amma zuciyar mai bayarwa. Idan zuciyarka ba ta tsarki a gaban Allah ba abin da za ka yi da zai gamshe Shi. Babu yadda za ka yi wa Allah ibada da kazantaccen abu. Misali ba za ka iya satar kudin jama’a, kudin gwamnati ba, ka yi wani abu da shi Allah Ya ji dadi ba; koda Masujada ka gina ba zai ba ka lada ko kadan ba, sai dai la’ana daga wurin Allah.
Wani lokaci yaya kake yin tunani a zuciyarka idan Ubangiji Allah Ya albarkaci makwabcinka? Sau da dama mutane sukan ji haushi don ba su ba ne suka sami wannan alfarma, suna kishin wanda ya samu; irin wadannan mutane za su yi murna kwarai idan suka ji cewa ka shiga cikin wata irin wahala ko kuwa wani irin bala’i ya auko maka. Idan suna da zarafi, za su iya kashe ka. Wannan ba daga wurin Allah ba ne. Duk mutumin da ya bar bin sharidun Ubangiji Allah, zai iya aikata kowace irin mugunta.
Mutum ya soma aure biyu:
Lokacin da Allah Ya halicci mutum Ya sa shi a cikin gonar Adnin, Allah ne da kanSa Ya ga namiji na da bukatar mataimakiya, a lokacin ne ya yi Hawa’u matarsa ya kawo ta gare shi, ita kadai guda daya. Ba abu mai wuya ba ne a wurin Allah idan yana son miji ya zama da mace fiye da daya, da tun a lokacin zai yi masa mata yadda Yake so; amma ba haka ne Ya yi ba! Mu sake dubawa: “Ubangiji Allah kuma Ya ce, ba ya yi kyau ba mutum ya kasance shi daya; sai in yi masa mataimaki mai dacewa da shi………….Sai Ubangiji Allah Ya sa barci mai nauyi ya dauki mutumin, ya kuwa yi barci, Ya dauki daya daga cikin hakarkarinsa, ya toshe wurin da nama maimakonsa: hakarkarin kuwa, wanda Ubangiji Allah Ya dauka daga cikin mutumin, Ya maishe shi mace, Ya kawo ta wurin mutumin. Mutumin kuwa ya ce, Wannan yanzu kashi ne daga kasusuwana, nama ne daga namana, za a ce da ita mace domin daga jikin namiji aka ciro ta.” (Farawa 2 : 18, 21 – 23).
Shirin Allah a cikin gonar Adnin ga mutum shine, ya zauna da matarsa daya; idan muka lura, akwai kasusuwa da yawa a hakarkarin mutum, amma Allah Ya cire guda daya ne kawai domin ya gyara mace da shi. Da Allah Ya fitar da mutum daga cikin gonar Adnin sai muka soma ganin auren mata biyu har ma fiye da biyu: “Lamec ya auri mata biyu: sunan dayan Adah ne, na dayan kuma Zillah.” (Farawa 4 : 19). Farkon auren mata biyu ke nan a duniya.
Lokacin da Yesu Almasihu ya ke koyarwa, sai wadansu suka zo da tambaya a gare shi: “Sai wadansu Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce, ko halal ne ga mutum shi saki matatasa saboda kowane irin sanadi? Ya amsa, ya ce, Ba ku karanta ba shi Wanda Ya yi su tun farko, namiji da ta-mata Ya yi su, har Ya ce Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne wa matatasa; su biyu kuwa za su zama nama daya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama daya ne. Abin da Allah Ya gama fa kada mutum shi raba. Suka ce masa, don mene ne fa Musa ya hukunta a bada takarda ta kisan aure a sake ta kuma? Ya ce masu, domin taurin zuciyarku Musa ya bar ku ku saki matanku: amma ba haka yake a farko ba.”(Matta 19: 3-8).