Mutanen wata al’umma masunta a Jihar Taraba sun yi fice wajen yin nutso su shiga can kasan ruwa na tsawon sama da awa daya ba tare da sun dago sun shaki numfashi ba.
Wadannan masunta, sun gaji lakaninsu ne daga wurin iyaye da kakanni tun shekaru aru-aru, sannan kuma da sana’arsu ta kamun kifi suke dogaro.
- Yanzu garau nake, inji Tinubu bayan jinyar wata uku a Birtaniya
- An bankado shirin masu neman tada fitina a zaben Filato
Tun yaro yana jinjiri masuntan suke jefa shi cikin ruwa domin a shirya shi tun kafin ya girma ya tsunduma harkar su din gadan-gadan; har yanzu kuma ba su daina yin wannan al’adar ba shekaru aru-aru ba.
Wani abin mamaki game da su shi ne ba yarensu daya ba — al’ummar ta hada kabilu daban-daban masu bambancin addini — amma kuma al’adunsu daya.
Wadannan kabilu sun hada da Kabawa, Jiru, Wurbu Jukun Wanu, Kakanda, Burkani da dai sauransu, kuma suna zaune ne a gabar kogin da ya tashi daga Binuwai, ya tafi zuwa Taraba ya dangana da Donga da ma wasu sassan jihar Taraban.
Mutanen ba su yarda sun saki al’adunsu ba, kuma duk da cewa ba addininsu daya ba, hakan bai sa al’adunsu sun bambanta ba.
Kazalika bayan su, sukan yi fiton mutane da kaya, wasunsu kuma sukan bayar da maganin gargajiya.
Wakilin Aminiya ya yi tattaki domin gane wa idonsa wannan al’umma mai abun al’ajabi, inda ya fara kicibis da Mayoreniwo, wani babban garin masuntan mai babbar kasuwar kifi a kan babbar hanyar Jalingo zuwa Wukari a Jihar Taraba.
Wakilin namu ya samu damar zantawa da shugaban riko na masu fito na duk fadin Jihar Taraba, Alhaji Jidda Sulaiman, wanda ya kewaya da shi zuwa wurare da dama a cikin ruwan bisa jirgin ruwa tare da kuma nuna mishi yadda suke gudanar da ayyukansu na fito.
– Sana’ar su ita ce rayuwarmu
Baya ga haka, wakilinmu ya samu tattaunawa da wasu fitattun masuntan yankin da ke iya yin awanni a cikin ruwa ba tare da sun dago domin shakar numfashi ba.
Daya daga cikinsu, Musa Basho, mai shekara 70, ya shaida mana cewa ya fara su ne tun yana da shekara 9 a duniya, kuma tun daga lokacin ba shi da wani aiki in ban da su din.
“Nakan yi nutson sama da awa daya ba tare da dagowa domin shakar numfashi ba, wannan ya sa ake kiran mu domin kawo agajin gaggawa a duk lokacin da aka samu kifewar jirgi ko kuma neman gawa a cikin ruwa.” a cewar Basho.
Ya shaida wa wakilinmu cewa wata mota ta taba fadawa a cikin kogi daga kan gadar Numan, duk fasinjojin cikinta suka rasu kuma su ka bace, sai da aka kira mu, ’yan Mayereyo sannan muka gano gawarwakin.
Bulus Dauda, mai shekara 30, shima daya ne daga cikin masuntan da suka yi fice a kauyen.
Ya shaida mana cewa ya fara sana’ar su tun yana dan shekara bakwai, tun yana dan karami ba shi da wani aiki da ya wuce kamun kifi kuma ya sha kwana cikin kwale-kwale saboda aiki.
Ya kara da cewa ba a iya ruwan garin nasu suke gwada bajintar tasu ba, a lokuta da dama sukan tafi wasu garuruwan domin nuna bajintarsu ta iya su, har a wurare kamar Makurdi da Lokoja, har zuwa Kalaba.
– Arangama da ’yan ruwa
“A wasu lokutan idan muna aiki da dare mukan yi arangama da ’yan ruwa, amma hakan ba ya hana mu ci gaba da aikinmu,” inji shi.
Shi ma wani masunci a garin Zip da ke kan gabar kogin Biniwai, Zubairu Zakari Bakabe, ya ce yana iya yin nutso na sama da awa daya da rabi a ruwan idan bukatar hakan ta taso, kuma ya gaji lakaninsa ne daga wurin kakannnisa.
Ya ce duk lokacin da aka samu wani ya fada ruwa su ake kira su kai dauki tun daga yankin Kwantan Nanido har zuwa Kambari da Amar.
– Kabawa sun fi gwanancewa
A cikin dukkannin al’ummomin masunta mazauna gabar ruwan da muka gana da su al’ummar Kabawa sun yin fice da gwanacewa wajen yin su da sauran aubuwan a ruwa, ba a Najeriya ba, har a wasu kasashen Gabas da Yammacin Africa.
Asalin Kabawa mutanen Argungu ne a Jihar Kebbi, amma sun watsu a dukkanin sassan Najeriya, kuma ana ganin cewa duk abun ya gagaresu a ruwa, to babu wata kabila da za ta iya yin shi.
– Sirrin masuntan
Aminiya ta gano cewa masuntan na da wani sirri da ba su fada wa kowa koda kuwa dan uwansu masunci ce, saboda sun yi amannar cewa duk wanda ya fadi sirrin zai iya rasuwa, dangin da ya fito kuma za su rasa wannan lakanin gaba daya.
Shi ma Maigarin Zip, ya shaida mana cewa lakanin nasu ba su fada wa kowa saboda sirrinsu ne.
Ya kara da cewa ba don irin lakanin nasu ba, da ba za su iya aikin nasu ba.
Ya ce akwai wata rana suna su da tsakar dare sai ga jariri rayayye a cikin kallin da suke su din da shi;
Abin da suka yi kawai shi ne cire jaririn suka mayar da shi cikin ruwa saboda sun san sharrin ’yan ruwan ne, kuma ba abin da ya faru daga baya.
Bayan nan sau tari ’yan ruwan kan yi yunkurin su razana su amma saboda a shirye suke ba sa wani razana.