✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin wutar lantarki ya tilastawa kotu taƙaita zamanta na awa 3 a Kano

Kotun ta taƙaita zamanta zuwa awanni uku a rana saboda tsadar man dizal.

Sanadiyyar matsalar rashin wutar lantarki ta ƙasa da kuma sakamakon katsewar wutar lantarki da ta jefa wasu jihohin Arewa cikin duhu ba kawai ta janyo asarar dukiyoyin masu amfani da wutar lantarki ba kaɗai ba ne.

Wannan ci gaban rashin wutar ya tilastawa wata babbar kotun tarayya da ke Kano taƙaita zamanta zuwa awanni uku a rana saboda tsadar man dizal.

Kamfanin lantarkin ya ba da rahoton katsewar wutar a yankuna da dama na Arewa bayan layukan rarraba wutar lantarki mai ƙarfin kilo 330 na Ugwaji-Apir mai layi na 1 da 2 sun faɗi da misalin ƙarfe 4:53 na safe, lamarin da ya jawo damuwa ga mazauna yankin.

A lokacin da lauyoyi da masu ƙara suke zaman shari’a a ranar Alhamis da safe, Mai shari’a Simon Ameboda ya bayyana cewa kotun za ta zauna na tsawon sa’o’i 3 ne kawai ta dogara da janareta da ke bai wa kotun wutar lantarki ne.

Hakan ya sa aka dakatar da shari’o’in da ba su kai ga sauraren ƙorafi ba.

Wani ma’aikacin kotun da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, a ranar Laraba an kashe kuɗi Naira miliyan daya kan sayan dizal kaɗai.

A halin da ake ciki kuma, Kamfanin Rarraba wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ya ce jami’an da suke aiki kan layukan sa sun gano matsalar da ya haddasa matsalar wutar lantarki a layin Ugwuaji-Apir mai nauyin ƙarfin 330 (kV).

Kamfanin ya ba da rahoton katsewar wutar lantarki a yankuna da dama na Arewa bayan layukan rarraba wutar lantarki mai ƙarfin kilo 330 na Ugwaji–Apir mai lamba 1 da 2 sun ci karo da juna, lamarin da ya jawo damuwa ga mazauna yankin.

Amma Babban Manajan Hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya ce an gano matsalar ne a yankin Igumale da ke Jihar Benuwe.