Daruruwan yara ’yan makaranta a kauyen Gadawa da kauyukan da ke makwabtaka da shi a Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina, sun daina zuwa makaranta bayan da sojoji suka yi sansani a makarantarsu ta firamare.
Bayan hari da aka sace dalibai sama da 300 a sakandaren Kankara da kuma hare-haren ’yan ta’adda a kananan hukumomin Danmusa da Dutsinma, rundunar sojojin ta ajiye sansaninta a yankin domin dakile matsalar tsaro.
Kauyen Gadawa da ke Karamar Hukumar Danmusa yana kan titin Dutsinma zuwa Kankara ne, kuma ya zama wurin da ya fi dacewa da sansanin sojojin, inda suka mai da makarantar firamare ta Gadawa a matsayin sansaninsu.
Makarantar a cewar mazauna yankin, kafin yanzu tana da dalibai kusan 370 daga Gadawa da kauyukan da ke makwabtaka da ita.
Kuma karbe wurin da sojoji suka yi, ya tilasta wa dalibai da yawa barin makaranta.
Wasu daga cikin iyayen da ke da halin jigilar ’ya’yansu a yau da kullum zuwa makaranta, sun mayar da su wasu makarantu a ’Yantumaki da wasu garuruwa.
Sauran mazauna yankin da ba za su iya daukar dawainiyar kai ’ya’yansu zuwa wasu wuraren ba, sun yi kokari a matakin farko don ganin sun samu gurbin karatun ’ya’yan, amma kokarinsu bai je ko’ina ba.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin, ya gano cewa kimanin yara 70, wadanda kashi 20 ne cikin 100 na daliban, suna ci gaba da karatu a wani gidan laka da ba a kammala ba, wanda ba ya da rufi ko kofofi da tagogi, lamarin da ya sa yanayin karatunsu ya tabarbare.
Da tsakar rana ce, amma an riga an rufe makarantar ta wucin-gadi saboda yara ba za su iya yin karatu a cikin rana mai zafi ba, kuma kujerunsu na karfe sun yi zafi sosai.
Ginin wanda ke da dakuna uku kawai, bayan ba a kammala shi ba, ya yi kadan sosai wajen daukar dalibai 70 ba tate da matsatsi ba, don haka sai dai wasu su zauna a waje.
Da suke kokawa kan lamarin, wasu daga cikin iyayen yara sun bayyana takaicinsu inda suka ce sun yi ta kokarin kaiwa ga gwamnati domin neman agaji amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Malam Auwal Lawal, ya ce “A gaskiya muna da dalibai kusan 370 a makarantar, amma abin takaici mafi yawansu a yanzu suna yawo a titi, wasu kuma suna taimakon iyayensu ne kawai da tallace-tallace. “Gidan da yaranmu suke karatu a yanzu bai dace da makaranta ba, domin ginin ba ya da rufi, babu yadda za a yi yaran su zauna a cikin laka da damina.
A cikin wannan yanayi lokacin zafi kuma yara ba za su ji dadin zama a cikin ginin mai zafi ba.
Hakazalika, muna gab da shiga lokacin hunturu, don haka ba sai an yi bayani ba, ka san yadda wurin zai yi sanyi ba tare da rufin ba, kuma ba tare da kofofi da tagogi ba,” in ji shi.
Ya ce al’ummarsu tana cikin hadari a nan gaba ganin cewa yawancin ’ya’yyasu ba za su iya samun ingantaccen ilimi ba.
Sai dai ya ce al’ummar ba suna korafin kasancewar sojojin a yankinsu ba ne, domin suna taimakawa wajen dakile matsalar tsaro, sai dai kawai suna neman a samar wa ’ya’yansu makaranta ne.
“Gwamnati za ta iya samar da wani sansani ga sojojin a mayar mana da makarantarmu ko kuma a gina wata makarantar don yaranmu su yi karatu,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Tasi’u Umaru, ya ce abin takaici ne yadda wasu yaran da suka kammala makarantar firamare a yankin suka kasa rubuta sunayensu daidai saboda rashin samun kyakkyawar koyo da koyarwa.
“Mun yi kokarin samar da wurin wucin-gadi ga yaranmu. Da farko wani Sani Mai Lemo ya ba mu gidansa, amma ya yi zargin gwamnati ce ke biyan kudin hayar, kuma kudin ba ya zuwa gare shi, don haka ya kori yaran, ya ce suna lalata masa kofa da tagoginsa.
“Wani mai suna Malam Sabitu ya ba mu nasa gidan, amma daga baya ya yi aure ya tare a ciki.
“Daga nan sai muka yi rumfa ta wucin -gadi a bakin hanya, amma aka gargade mu cewa abin kunya ne a bangaren gwamnati idan aka ga yara suna koyo a irin wannan yanayi,” in ji shi.
Ya ce a karshe gidan da suka samu ba ya da rufi, kofofi, da tagogi da kuma isassun kujeru na dalibai, don haka ya yi kira ga gwamnatita kawo musu dauki.
Dayyanu Sani shi ne Sakataren Kungiyar Ci-gaban Matasan Gadawa, ya bayyana yadda suka yi ta kokarin tuntubar gwamnati domin neman agaji amma daga baya aka shaida musu cewa ba za su iya ganin Shugaban Sashen Ilimi na Karamar Hukumarsu don su kai kokensu ba.
“Da farko mun zauna a matakin kungiyarmu inda muka tattauna kan yadda za mu nemo mafita daga tabarbarewar karatun yaranmu.
“Daga nan muka kai maganar gaban dattawan gari, tare muka yanke shawarar kai maganar gaban hukumomin ilimi na Karamar Hukumar Danmusa bayan tuntubar malaman makarantar da abin ya shafa, amma abin takaici bayan kokarin da aka yi mun kasa samu mu gan shi,” in ji shi.
Ya nanata kiran ko dai a mayar da sansanin soji zuwa wani wurin da ke kewayen garin ko kuma a gina wata makaranta ga yaran.
Mai unguwar Gadawa ya ce ba zai iya cewa komai ba a kan lamarin ba tare da izini daga dagacinsu ba, wanda shi kuma sai ya samu izini daga hakimi.
Sai dai dan uwansa, Shitu Muhammad Gadawa, ya roki gwamnati ta gaggauta shiga lamarin.
“An ce bambancin wanda bai yi karatu da jaki ba shi ne rashin bindi. Don haka muna kira ga gwamnati ta duba wannan al’amari ta ceto ’ya’yanmu.
“Muna da ’ya’yan Gadawa a nan da ake kira Sabon Garin Dan’Ali, akwai kuma yara daga Gadawar Daji, wanda shi ne tsohon kauyen daga nan aka samu sunan kauyenmu, akwai kuma daliban kauyen Hawan Dan Maigyada da kuma dalibai daga rugagen Fulani da dama da ke kewayen wannan yanki da suke zuwa wannan makarantar firamare kafin a karbe ta.
“Yawancinsu a yanzu, musamman ’ya’yan Fulani sun daina karatu,” in ji shi.
Ya ce mafi yawan malaman ba sa kula da aikinsu sosai saboda rashin wurin da ya dace, yana mai zargin cewa babban abin da ke damunsu shi ne su zo su sanya hannu a kan rajista.
“Wasu daga cikin malaman suna shafe kwanaki ba tare da sun shiga aji don koyarwa ba. Suna sanya hannu ne kawai a rajistar su tafi don kada a kama su,” in ji shi.
“Ina kira ga gwamnati ta taimaka wa ’ya’yanmu domin idan babu ilimi, wasu daga cikinsu za su girma ne da wasu munanan dabi’u wadanda ba za su yi mana dadi ba,” in ji shi.
Kokarin jin ta bakin jami’an soji a sansanin ya ci tura yayin da suka yi ikirarin cewa shugabansu, wani Manjo a rundunar ba ya nan a lokacin, inda suka ce ya ta fi kauyen ’Yantumaki, kuma in ba tare da izininsa ba, ba za a iya yin komai ba.
Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Babangida Mu’azu kan lamarin, ya ce kasancewarsa sabo a ofishin, ba a yi masa bayani kan matsalar ba, amma ya yi alkawarin daukar mataki.
“Yanzu ke nan kake kawo min rahoton lamarin. Don haka zan yi magana da Kwamishinan Ilimi na matakin farko da na sakandare, daga nan ne za mu ga abin da za mu yi a kai,” in ji shi.