Wasu gungun matasa sun yi zanga-zanga a kofar Majalisar Dokoki ta Kasa, suna kira da a sauke mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno.
Matasan, wadanda ke karkashin wata kungiyar Majalisar Matasan Arewa sun gudanar da zanga-zangar ce a ranar Laraba.
- Mutum 7 ’yan gida daya sun rasu bayan cin Dambu mai guba a Zamfara
- Bidiyona da ake yadawa a kan Buhari tsoho ne, yanzu ba na tare da shi – Nata’ala
Sun ce suna yinta ne bisa dalilin cewa Manjo Janar Monguno (mai ritaya), ya gaza wajen magance matsalar tsaro a kasar a matsayinsa na mai ba shugaba Buhari shawara kan harkar.
Matasan suna mai cewa rashin tabuka komai game da tsaron na gwamnantin Buhari ba zai rasa nasaba da rashin mashawarata na gari da ya rasa ba, ganin cewa a karkashin kulawar Monguno ’yan ta’adda sun kara karfi.
Matasan sun ce karfin ’yan ta’addan ya kai sun hakala zaratan sojojin Fadar Shugaban Kasa, suka kuma yi barazanar kama Buharin da Gwamnan Kaduna, Nasiri El-Rufa’i.
A jawabinsa ga ‘yan jarida, Sakataren kungiyar ya ce “La’akari da yadda ake kisa da kuma sace ’yan Najeriya a gidajensu da gonaki da kuma manyan hanyoyin kasar nan, hakan ya kara haddasa fatara da kuncin rayuwa”.
“Haka ma a kudancin kasar nan, an hana jama’a fitowa a ranakun Litinin don neman abinci wanda ke nuna nakasu a tsarin samar da tsaro a kasar nan, a inda ‘ynan bindiga ke cin karensu ba babbaka,” inji shugaban kungiyar.
Wadanan duk na nuna gazawar mai ba shugaban kasa shawarar ne, ko kuma shawarwarinsa ba sa aiki yadda ya kamata, don haka shugaba Buhari ya gaggauta sauke shi tare da nada wanda ya dace.
Idan za a iya tunawa, Shugaba Buhari ya sake nada Monguno ne lokacin da ya sauke Tukur Burutai da Sadique Abubakar da sauran manya-manyan hafsoshin tsaron kasar sakamamkon kasa magance matsalar tsaro.