Fitaccan malamin Musulunci a Najeriya, Sheik Dahiru Usman Bauchi, ya ce ’yan kasar suna cikin fargaba saboda babu wanda ya tsira a cikin daga matsalar tsaron da ke addabar kasar.
Malamin ya ce ’yan kasar ba su taba tsanmanin za su tsinci kansu a makamancin halin da kasar take ciki a yanzu ba, alhali akwai gwamnati wadda alhakin kare su da samar musu tsaro ya rataya a wuyanta.
- Matasa sun kona ofishin ’yan sanda a Sakkwato
- An sako daliban jami’ar da aka sace a Makurdi
- Ya halasta mai azumi ya sha abun kara kuzari —Sheik Lawan Abubakar
“Idan kana gida ba ka tsira ba, a hanya ma ba ka tsira ba, amma har yanzu gwamnati ta gaza fitar da mu daga wannan tashin hankali na ba gaira babu dalili,” inji shehin malamin.
Da yake yake karbar bakuncin wakilan Kiristoci bisa jagorancin tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung da Fasto Yohana Buru na Kungiyar Samar da Daidaito da Zaman Lafiya a Najeriya, Sheik Dahiru Bauchi ya ce rashin tsaro da Najeriya take ciki abun tsoro da ban takaici ne.
“Mun yi tsammani matakan gwamnati uku —Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi— za su fitar da mu daga matsalolin da muke fama da su, amma yanzu babu wanda ya kubuta daga cikinmu.
“Ba mu zabe su ba don su jefa mu cikin wannan hali ba, ko don su sayar da mu kamar dabbobi, ko su rika tafiyar da al’amuran kasa yadda suka ga dama ba, alhali akwai gwamnati a kasa.
Ya jaddada cewa a matsayin Gwamnati na mai alhakin kare rayukan jama’ar Najeriya, wajibinta ne ta tashi tsaye ta magance ayyukan ’yan bindiga da sauran nau’ikan ta’addanci.
“Muna sane cewa gwamnati ta san halin da kasar nan ke ciki, da duk abun da ke faruwa, haka su ma gwamnonin da shugabannin kananan hukumomi.
“Saboda haka, ya kamata su sani, su kuma saurari kokenmu, domin mutane ba sa iya zuwa kasuwa saboda tsoron kada a yi musu kisan gilla.
“Wajibi gwamnatin Najeriya ne ta yi wa ’yan kasar abun da suke bukata na kare Musulminsu da Kiristoci daga hare-haren ’yan ta’adda.”
A nasa jawabin, Solomon Dalung ya ce, sun kawo ziyarci Sheik Dahiru ne domin su yi buda-baki da shi, da kuma neman ya sanya Najeriya cikin addu’o’insa.