A makon da ya gabata ne wata tawaga daga Sashen Kula da kananan Hukumomi dake ofisihin sakataren gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mista Kayode Adebayo su ka ziyarci karamar hukumar Kagarko dake Kudancin Jihar Kaduna don ganewa idonsu abubuwan da karamar hukumar ta samu da kuma aiwatarwa.
Wannan rangadi, wanda makasudinsa shi ne fitar da karamar hukumar da ta fi gabatar tare da aiwatar da aikace-aikace a yankinta. “Manufar wannan ziyara shi ne mu ganewa idanunmu don zabar karamar hukumar da ta fi zartar da ayyukan taimakon jama’a.
“Har ila yau kuma ta hanyar wannan tantancewa ce zamu gane irin karfin haraji na cikin gida da kowace karamar hukuma ke samu da kuma irin karfin dogaronta da asusun gwamnatin tarayya,” in ji shi
Sadda yake maida jawabi, Kantoman karmar Hukumar Kagarko, Alhaji Kabir Yusuf wanda shugaban sashen gunarawa na karamar hukumar, Alhaji Sani Bello ya wakilta ya bayyana cewa karamar hukumar ta yi nasarar aiwatar da ayyuka 11 daga cikin guda 20 da ta dauko tun shekarar 2015.
Yusuf, ya kara da cewa duk da rashin samun cikakken cin gashin kai da karamar hukuma ke da shi amma sun yi kokari sun tabuka abin a zo a gani karamar hukumar. A karshe ya yabawa gwaman jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i bisa ga irin goyon bayan da yake baiwa karamar hiukumar da sauran kananan hukumomin jihar.