Kocin kulob din Manchester City da ke Ingila Manuel Pellegrini ya ce yana da yakinin kulob din zai murmure daga rashin nasarar da ya samu daga wajen kulob din Chelsea da hakan zai ba shi damar lashe kofin a karshen kakar wasa ta bana.
A wasan da kungiyoyin kwallon kafar biyu suka yi a ranar Litinin da ta wuce kulob din Chelsea ya bi na City har gida ne ya doke shi da shi daya mai ban haushi da hakan ta sa kowannensu ya hada maki 53 daga wasanni 24.
Ya zuwa yanzu kulob din Arsenal ne yake samun tebur a gasar da maki 55 sai Manchester City a matsayin ta biyu yayin da Chelsea kuma ke matsayi na uku.
Kocin City, Pellegrini ya ce duk da yake sun samu rashin nasara a wasan yana da tabbacin kulob dinsa ne zai lashe kofin Premier a kakar wasa ta bana.
Masu iya magana dai sun ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
Rashin nasarar da muka samu a wasanmu da Chelsea ba zai hana mu lashe kofin Premier ba -Pellegrini
Kocin kulob din Manchester City da ke Ingila Manuel Pellegrini ya ce yana da yakinin kulob din zai murmure daga rashin nasarar da ya samu…
