✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin man fetur ya sa ’yan bindiga sun koma amfani da rakuma a Sakkwato

Mazauna yankunan sun ce yanzu a kan rakuma ake kai musu hari.

Shiga halin tsaka mai wuyar da ’yan bindiga suka yi sakamakon hana sayar da man fetur a jarkoki a Jihar Sakkwato ya sa yanzu ala tilas sun koma amfani da rakuma wajen zirga-zirga.

A cikin kusan mako daya, ’yan sanda sun kama mutane da dama da ake zargi da fasakwaurin man fetur ga ’yan bindiga zuwa cikin dazuka a sassa da dama na Jihar ta Sakkwato.

Akalla Gwamnoni uku ne a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya suka kakaba dokar haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki don magance kaulubalen tsaron da ayyukan ’yan bindigar ya haifar.

Wani mazaunin Sakkwato wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ’yan bindigar da ke yin kaura zuwa Jihar daga Zamfara, yanzu sun fara kafa sansanoni a dajin Isa da ke Jihar bayan kasurgumin dan bindigar nan, Turji, ya gayyace su.

Ya ce yanzu haka, akwai akalla gungu 20 na ’yan bindigar a yankin, kuma dukkansu sun zo ne a kan rakuma saboda babu damar tuka babura saboda rashin man fetur.

Majiyar, har ila yau ta ce ’yan bindigar kan yi amfani da rakuman wajen kai hari kan yankunan nasu da kuma satar mutane.

Sai dai Kwamishinan Tsaro na Jihar, Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya ce babu wata hujja da ke nuna ’yan bindigar na karkafa sasanoni a yankin.