✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin aikin yi ka iya ruguza Najeriya —Ministan Kwadago

Ministan ya ce dole a samar wa mutane ayyukan yi in har ana son kawo karshen matsalar tsaro.

Ministan Kwadago da Ayyukan Yi,  Chris Ngige, ya ce karuwar rashin aiki na ci gaba da zame wa Najeriya babbar barazana da iya rusa kasar baki daya.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata, yana mai alakanta matsalar da rashin ilimi wanda ke ci gaba da ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Mista Ngige ya ce, “Muna cikin matsala a kasar nan. Muna cikin matsala kuma duk wanda ya gaya muku cewa bai san muna cikin matsala ba, to karya yake yi wa kansa.

“Ya rage gare mu ni da ku da wadanda ake damawa da su, mu yi shawarar yadda za mu ceci kanmu, da ‘ya’yanmu da kasarmu baki daya.

“Idan muka ci gaba da tafiya a kan wannan hali da ake ciki – sayen harsasai da dasa wa mutane bam – to asarar kudi da lokaci za a ci gaba da yi.

“Amma idan ka dauki matakan kariya, ba za ka yi asarar kudi sosai ba. Dole mu bai wa mutanen nan ilimi tun daga tushe.

“Wadanda ba su da hanyar samun ilimi kuma, dole mu ba su ayyukan yi don su dogara da kans, su rufa wa kansu asiri.”