Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya bayyana cewa ko shakka babu Amurkawa na sha’awar zuba jari a Najeriya, amma tarin matsaloli ke hana su iya aikata hakan.
Blinken ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga manema labarai bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja a ranar Talata.
- An sace magidanci da matarsa da ’ya’yansu a Kaduna
- Sojoji sun kwato mutane daga maboyar ’yan bindiga a Kebbi
A cewar Blinken, matsaloli masu alaka da rashawa baya ga wahalar canjin kudade su ne manyan dalilan da ke dakile masu zuba jari na Amurka iya gudanar da hada-hadarsu a Najeriya.
A jawabin wanda Blinken ya yi kafada-da-kafada da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa matuƙar Najeriya na fatan samun zuba jari na kai tsaye tare da shigowar kamfanoni, ko shakka babu sai ta yi aiki tukuru wajen magance matsalar cin hanci da rashawa wadanda za su buɗe hanya ga masu zuba jari su iya sauya kuɗaɗensu cikin sauƙi.
Blinken wanda ya yaba wa yanayin tattalin arziki Najeriya, ya ce muddin aka magance matsalolin da ke firgita masu zuba jari, za a ci moriya mai tarin yawa musamman a fannin musayar fasahohi da kasuwanci.
Najeriya ce ƙasa ta uku da Blinken ke ziyarta a rangadin da yake yi zuwa ƙasashen Yammacin Afirka da zimmar ganin ɗorewar tasirin Amurka a Afirka.
Sauran kasashen da Mista Blinken ke ziyarta sun haɗa da Cape Verde da Ivory Coast da kuma Angola.