✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kwato mutane daga maboyar ’yan bindiga a Kebbi 

Kun kashe dan bindiga sannan suka kwato makamai daga maboyar ’yan bindiga

Jami’an tsaron sun kashe wani dan bindiga suka kwato mutane hudu a wata maboyar ’yan bindiga da ke kauyen Sabon Gari a Karamar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.

Sojoji da hadin guiwar sibil difens da ’yan banga sun kwato makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda uku da wasu kananan bindigogi da harsasai na musamman guda 142, da kakin sojoji guda biyu.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Birged ta Daya ta Sojin Kasa da ke Gusau, Kyaftin Yahaya Ibrahim ya ce a lokacin farmakin, sojojin sun hallaka dan bindiga daya, sannan suka kubutar da mutum hudu da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar da ya fitar ta ce dukkan mutum hudun maza ne, tuni an sada su da danginsu, kuma jami’an tsaron sun cigaba da farautar ’yan bindigan da suka tsere.