Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce shi da kansa zai jagoranci gwajin makaman Nukiliya mallakin kasarsa a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dardar kan fargabar kasarsa za ta mamaye Ukraine.
Za a gudanar da gwajin makaman ne ranar Asabar, kamar yadda Ma’aikatar Tsaron Rasha ta tabbatar, inda ta ce gwajin zai kuma kunshi makamai masu cin dogo da matsakaicin zango.
- An cafke matar da ta jima tana buga jabun kudi a Ogun
- An ceto daruruwan mutane a jirgin ruwa da ya kama wuta
Shugaban Kasar Belarus, Alexander Lukashenko, yayin wata tattaunawarsa da Putin ranar Juma’a ya ce shi ma zai bi sahunsa wajen kallon gwajin makaman.
Gwajin dai zai zo ne bayan a ranar Alhamis Shugaban Amurka, Joe Biden, ya yi gargadin cewa Rasha na iya mamaye Ukraine cikin ’yan kwanaki masu zuwa.
Kasashen Yamma dai sun bayyana fargabar cewa akwai akalla dakaru 190,000 da Rasha ta jibge a kan iyakarta da Ukraine.
Rasha dai ta sha nanata cewa ba ta da aniyar mamaye Ukraine, ko da yake ta sha gargadin Amurka da kawayenta kan su janye dakarunsu da ke cikin Kungiyar Kwance ta NATO daga yankin Gabashin Turai.
Amurka dai ta yi watsi da bukatun na Rasha, ko da yake Putin ya yi barazanar daukar matakin soji matukar kasashen Yamman suka ci gaba da girke dakarunsu a yankin.
Kakakin gwamnatin Ukraine, Dmitry Peskov, ya ce tuni kasar ta Rasha ta sanar da mutanen yankin da za a yi gwajin kuma za ta yi komai a bude ne, inda ta shawarce su da kada su tsorata.