Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi alkawarin taimaka wa Najeriya wajen yakar ta’addanci da kuma masu tsattsauran ra’ayin addini.
Ya bayyana haka ne yayin da ya ke karbar bakuncin Jakadan Najeriya a kasar, Farfesa Abdullahi Y. Shehu wanda ya mika masa takardar fara aiki a fadar Krelim.
- Masu garkuwa da mutane sun bukaci Sigari da Tabar Wiwi a matsayin fansa
- An gano gawar da ta shafe shekara 800 hannayenta na rufe da fuskarta
Putin, ya kuma jadadda aniyarsa ta ci gaba da yaki da ta’addanci a fadin duniya.
Ya ce, kasarsa za ta martaba duk wata kasa da take da alaka da ita wajen tallafa mata ta fuskantar matsalar tsaro, don karfafa alakar da ke tsakaninsu.
Kazalika, Putin ya yi karin haske kan yadda COVID-19 ta kawo tsaiko a duniya, tare da cewar kasar shi ta kammala samar da rigakafin allurar cutar wadda za a yi amfani da shi wajen dakile cutar.
Shugaban, ya bayyana aniyarsa na kulla yarjejeniya da kowace kasa da ke shirin amsar rigakafin COVID-19 da kasar ta shi ta samar.
Da ya ke nasa jawabin, Jakadan na Najeriya ya nuna jin dadinsa kan irin alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma aike da sakon gaisuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga Shugaban na Rasha.