Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami a kan Kyiv, babban birnin makwabciyarta, Ukraine.
A ranar Alhamis ne dakarun Rasha suka yi wa birnin Kyiv luguden wuta, a karon farko cikin makonni.
Rahotanni sun ce hare-haren sun yi barna kuma Hukumar tara bayanan sirri ta sojojin Birtaniya an zargin rundunar Wagner group ya kai sabon harin.
Harkokin sun fara komawa yadda aka saba a Kyiv, bayan gazawar sojojin Rasha su kwace birnin a farkon lokacin da suka kaddamar da mamayar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
An kai sabon harin ne washegarin bikin zagayowar ranar samun ’yacin Ukraine, a daidai kuma lokacin da Shugaban Kasar Lithuanian, Gitanas Nauseda, yake ziyarar aiki a birnin Kyiv.
Rokokin Rasha guda 10 sun yi barna a yankin Chernihiv da ke Arewa maso Yammacin Kyiv a ranar Alhamis, kamar yadda gwamnan, Vyacheslav Chausov ya bayyana.
Rundunar sojin kasa da ke Arewacin Ukraine ta ce makamai masu linzami kusan 20 ne aka harbo daga yankin kasar Belarus zuwa Lardin Chernihiv, mai iyaka da kasar Rasha.