Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta sanya wa wasu ’yan Majalisar Dokokin Birtaniya 287 takunkumi bisa zargin su da tunzura al’umma su kyamaci Rasha.
Wannan matakin na nufin ’yan majalisa 213 daga jam’iyyar Conservative da 74 daga jam’iyyar Labour ba za su samu izinin shiga Rasha ba.
- Buhari zai yi buda-baki da su Tinubu a fadarsa ranar Talata
- Mutum 200 sun mutu a wani sabon rikici a Sudan
Ma’aikatar ta kuma ce tana iya daukan wasu matakan ladabtarwa, bayan da Birtaniya ta dauki irin wannan matakin a watan Maris.
Cikin jerin sunayen da Rasha ta fitar, akwai sunayen wasu ’yan majalisar da ba sa majalisar a halin yanzu.
Rashan ta dauki wannan mataki ne kan yadda kasashen Yammacin Turai ke nuna kyama da la’antar mamayar da ta Rasha ta yi wa Ukraine.
Tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, kasashe da dama daga Turai suka shiga sanya mata takunkumi tare da katse huldar diflomasiyya da ita.
Lamarin ya jefa tattalin arzikinta cikin wani mawuyacin hali.
A baya-bayan nan Birtaniya ta sanya wa manyan sojoji da attajiran Rasha takunkumi; ciki har da mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich.
Bayan sanya mishi takunkumi, Birtaniya ta kwace manyan kadarorinsa da ya mallaka a kasar, lamarin da ya tilasta sanya Chelsea a kasuwa.