✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da aka haifa ‘babu mahaifa’ ta haihu

Grace Davidson, mai shekara 36, an haife ta ne ba tare da mahaifar da za ta iya renon ciki ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, an haifi wata ‘yar baiwa a Birtaniya ba tare da mahaifa ba.

Mahaifiyar jaririyar mai suna Grace Davidson, mai shekara 36, tun farko an haife ta ne ba tare da mahaifar da za ta iya renon ciki ba.

A shekara ta 2023 ’yar’uwarta ta ba ta gudunmawar mahaifa – lamarin da ya zamo karo na farko a Birtaniya da aka yi dashen mahaifa cikin nasara.

Shekara biyu bayan wannan dashe, Grace ta haifi ɗiyarta ta farko a watan Fabarairun da ya gabata.

Ita da mijinta Angus, mai shekara 37 sun sanya wa jaririyar suna Amy, wato sunan yayar Grace, wadda ita ce ta bai wa ’yar’uwar tata mahaifar.

Grace mahaifiyar Amy, mai nauyin kilo biyu ta ce, ba za ta iya bayyana irin farin cikin da take ji sakamakon zama uwa a karon farko.

Grace da mijinta Angus, waɗanda ’yan asalin Scotland ne, amma suna zaune a birnin Landan, na sa ran samun haihuwa ta biyu nan ba da jimawa ba da mahaifar da aka ba su gudunmawa.

A farko, ma’auratan ba su so, su fito fili, su bayyana kansu ba, amma bayan haihuwar Amy, sun yanke shawarar tattaunawa da BBC kan abin da suka kira “ ‘yar baiwa”.

Likitocin da suka yi wa Grace aikin dashen mahaifar sun ce, sun kara yin irin wannan dashe sau uku ta hanyar amfani da mahaifar mutanen da suka mutu, tun bayan aikin da suka yi wa Grace.

Sun ce, suna sa ran yin dashen maihaifa 15 a matakin gwaji.

An haifi Grace ne da wata lalura da ba a cika samu ba, wadda ake kira MayerRokitansky-Küster-Hauser (MRKH) syndrome, inda mace kan zo babu mahaifa kwatakwata ko kuma ko da akwai mahaifar ba cikakkiya ba ce, sai dai sukan zo da kwayayan haihuwa.

A karon farko da BBC ta tattauna da ita a shekarar 2018, Grace na sa ran mahaifiyarta za ta ba ta mahaifarta domin ta samu damar haihuwa – sai dai daga baya an gano cewa, mahaifar mahaifiyar tata ba ta yi daidai da jikin Grace ba.

A shekarar 2019, BBC ta sake tattaunawa da Grace da mijinta Angus, lokacin da ake auna ’yar’uwar Grace, wato Amy Purdie, domin gano ko mahaifarta za ta yi wa Grace.

 Amy da mijinta sun riga sun haifi ‘ya’ya biyu, kuma ba su da bukatar kara haihuwa.

An zaunar da ’yan’uwan biyu, inda aka yi masu bayani dalladalla gabanin tiyatar dashen mahaifar.

Grace ta ce, an yi mata tayin amfani da tsarin dakon juna-biyu ko kuma ta karbi rikon yara, amma sai ta ga daukar jinjirin da ta rena a cikinta “abu ne mai matukar muhimmanci”.

“Na kasance ina son zama uwa,” in ji ta, “amma sai na rika dannewa a raina saboda halin da nake ciki.”

Haihuwa ta farko da aka samu bayan yin dashen mahaifa a duniya ta faru ne a kasar Sweden a shekarar 2014.

Tun daga wancan lokacin an yi dashen mahaifa kimanin sau 135 a fiye da kasashe 10, ciki har da Amurka da China da Faransa da Jamus da Indiya da kuma Turkiyya.

Haka kuma an haifi jarirai kimanin 65 bayan dashen. Kimanin likitoci 30 ne suka yi aiki a kan Grace lokacin dashen mahaifar da aka yi mata a watan Fabarairun 2023, inda suka kwashe sa’o’i 17 suna aikin cire mahaifar daga jikin Amy tare da mayar da ita jikin Grace.

An haifi jaririya Amy ne ta hanyar tiyata a asibitin Kueen Charlotte’s da ke yammacin birnin Landan a ranar 27 ga watan Fabarairu.

Grace da Angus sun ce, suna sa ran samun da na biyu – da zarar jami’an lafiya sun ce masu za ta iya sake ɗaukan ciki.

Za a cire mahaifar da zarar Grace ta haihu sau biyu.

Hakan zai bai wa Grace damar daina shan maganin da take yi a kullu-yaumin, wanda ke hana jikinta botsare wa mahaifar da aka dasa mata.