Rasha ta samu Dala biliyan 24 daga sayar wa kasashen China da Indiya iskar gas a cikin wata uku da ta auka wa makwabciyarta Ukraine da yaki.
Lamarin da ke nuni da yadda hauhawar farashin kayayyaki a duniya ke takaita kokarin da Amurka da Turai ke yi na hukunta Shugaba Vladimir Putin.
- NAJERIYA A YAU: Harin Gidan Yarin Kuje: ’Yar Manuniya Ta Nuna
- Mahara sun kashe dan sanda da sace dan kasar waje a Kwara
Bayanai sun nuna China ta kashe akalla Dala biliyan 18.9 wajen sayen iskar gas da gawayin daga Rasha a cikin wata uku kacal.
Kazalika, a tsawon lokacin, Indiya ta kashe Dala biliyan 5.1 wajen sayen iskar gas din daga Rasha, wanda hakan ya ninka har sau biyar na abin da ta kashe a bara.
Da wannan, Rasha ta samu karin kudin shiga na Dala biliyan 13 daga kasashen biyu idan aka kwatanta da abin da ta samu a shekarar da ta gabata.
Yawan sayayyar da kasashen ke yi daga Rasha na taimakawa wajen rage yin sayayya a wajen Amurka da ma wasu kasashen da suka dakatar ko jinkirta sayayyar don azabtar da Rasha dangane da yakin da take da Ukraine.
Haramcin ya sanya farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabo da kuma haifar da mishkila ga hauhawar farashin kayayyaki da ke barazana ga manyan fannonin tattalin arzikin kasar.
A cewar Lauri Myllyvirta, babban mai fashin baki kan harkokin makamashi, “A halin da ake ciki, China na sayen duk wani abu da Rasha ke fitarwa zuwa ketare ta bututu da kuma ta ruwa.
“Yayin da ita kuma Indiya ta kasance kan gaba wajen sayen mayan jiragen ruwan da Turai ba ta da bukatar su,” inji shi.