Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da soma yaki da kai farmakin sojojinsa na musamman a yankin Donbas da ke gabashin kasar Ukraine.
Putin ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye a talabijin, inda ya umarci sojojin Ukraine da ke gwabza fada tsakaninsu da ‘yan tawayen da Rasha ke goyon baya da su mika wuya.
- NAJERIYA A YAU: Da Bazar Wa Za A Yi Rawa A Sabuwar Tafiyar TNM?
- Karin kudin tikitin jirgin sama ya jawo karancin fasinjoji
Putin ya ce Rasha ba ta da niyyar mamaye Ukraine, amma idan aka fusata ta komai na iya faruwa.
Gwamnatin Ukraine ta ce yakin da Putin ya kaddamar ba komai ba ne face yakin son rai.
Yankin Donbas da ke kasar Ukraine dai wuri ne da mutanensa suka dade suna neman ballewa amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, lamarin da ya sa daga bisani suka nemi taimakon kasar Rasha.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Amurka da wasu kasashe za su mayar da martani mai zafi a kan harin da dakarun Rasha suka kaddamar a kan Ukraine.
Sai dai Putin ya yi gargadin cewa duk kasar da ta tsoma baki, yakin na iya shafarta.
Tuni kasashen duniya suka shiga sukar Rasha kan kaddamar da yakin, duk da sulhun da suka yi kokarin yi a tsakanin kasashen amma Putin ya yi kunnen uwar shegu.