Kasar Rasha ta gargadi kungiyar ECOWAS game da daukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Rasha ta bayyana cewa matakin da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ke shirin dauka zai iya haifar da rikicin da zai dade ba a ga karshensa ba.
- Babban Masallacin Zariya ya rufta kan masallata
- An yanke wa malama daurin shekara 600 saboda lalata da dalibi
Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta fitar ranar Juma’a, ta gargadi kasashen Yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar.
Sanarwar ta ce “Mun yi imanin cewa matakin soji ba zai warware matsalar Nijar ba, a maimakon haka lamarin zai haifar da mummunan rikici, wanda ba a san ranar karewarsa ba, tare da sake dagula lamura a yankin Sahel.”
Manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS na shirin wata ganawa a ranar Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.
A ranar Juma’a ne kungiyar ECOWAS ta amince da kafa ‘rundunar ko-ta-kwana’ a shirye-shiryen daukar matakin soji kan sojojin na Nijar.
Tuni dai shugaban kasar Ivory Coas, Alassane Ouattara, ya ce kasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 wadanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.
Kasashen Amurka da Faransa da kuma Tarayyar Turai tuni suka goyi bayan matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka, domin mayar da zababben shugaban kasar, Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
A ranar Juma’a magoya bayan sojojin na Nijar rike da tutar kasar Rasha suka gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin Jakadancin Faransa da ke birnin Yamai, inda suka rika kiran kasashen yamma su fice daga kasar tare da kira ga Rasha ta kawo musu dauki.
Har yanzu Rasha dai ba ta fito karara ta goyi bayan juyin mulkin na Nijar ba.
Kasashen Faransa da Amurka na da sansanonin soji a Nijar, domin yakar masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.