✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Masallacin Zariya ya rufta kan masallata

Mun lura da tsagewar ginin masallacin amma kafin mu dauki mataki wannan tsautsayi ya auku.

Akalla mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da dama suka jikkata sakamakon ruftawar wani sashe ne ginin Babban Masallacin Zariya da ke Fadar Zazzau a Jihar Kaduna.

Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda abun ya shafa suna tsaka da sallar La’asar ce yayin da ginin masallacin ya rufta kansu.

Sarki Bamalli ya ce tun a jiya Alhamis ce suka lura da yadda ginin masallacin ya tsage kuma suka shirya neman kwararrun injiniyoyin gine-gine domin yi wa tufkar hanci.

Sai dai ya ce tsautsayi wanda ba ya wuce ranarsa ya sanya wannan lamari ya faru tun gabanin a dauki matakin da ya dace.

“Tun a ranar Alhamis da ta gabata, aka sanar da ni labarin ganin alamar tsagewar gini a cikin masallacin, kuma da jin haka na umarci Barde Kerarriyar Zazzau [Haruna Idris] ya je don duba inda aka samu matsalar.

“Sai dai kuma ba ma inda ya tsage ne ya rushe ba, wani wuri ne na daban.”

A cewar Sarkin, “gini ne da ya dauki sama da shekaru 100 da gina shi, kuma lokaci daban-daban musamman lokacin damina ginin na yoyo.

“Lokacin da lamarin ya faru, mun dawo kenan daga buɗe wani masallacin Juma’a a garin Turawa da ke gundumar Soba, ya shiga gida kenan ba jimawa ake sanar da shi labarin.

“An samu gudunmawar jama’a da jami’an tsaro da kuma dukkanin hukumomin da ya kamata lokacin da lamarin ya faru”, a cewar Sarkin Zazzau.

Yayin da yake jajanta wa ’yan uwan wadanda lamarin ya shafa, Sarkin ya umarci a dawo gabatar da sallah a wajen masallacin har zuwa lokacin da za a kammala gyare-gyare.

Da yake karin haske kan lamarin, Abdulmumin Adamu, Sakataren shiyyar Zariya na kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross, ya ce, mutane da dama ne suka jikkata lokacin da lamarin ya faru, yayin da aka kai raka’a ta biyu ta Sallar La’asar.

Sai dai ya ce, akwai wanda ba su sami rauni sosai ba kuma tuni ma suka ci gaba da harkokinsu, yayin da wasu ke asibiti suna samun kulawar likitoci.

Baturen ’yan sanda na yankin, DPO Abdul Kasim mai kula da shiyar Zariya ya ce, “ya zuwa yanzu mutane 6 ne suka rasu, kuma mun mika gawarwakin ga ’yan uwansu.