✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 12 sun rasu, 28 sun ji rauni a hatsarin mota a hanyar Kano

An tabbatar da rasuwar mutane 12, wasu 28 sun ji rauni a sakamakon hatsarin wata tirela a kan hanyar Zariya zuwa Kano

An tabbatar da rasuwar mutane 12, wasu 28 sun ji rauni a sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Zariya zuwa Kano.

Hatsarin ya ritsa ne da wata tirela ce a kauyen Tashar Yari da misalin karfe 7.36 na safiyar ranar Litinin.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri, daukar akia fiye da kima.

An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin kula da lafiyarsu, amma dirban tirela na cikin wadanda suka rasu.

Kwamandan hukumar na Jihar Kaduna, Kabir Nadabo ya cewa, “Ina kira ga masu ababen hawa da su kasance masu yin tuki cikin aminci musamman a kan manyan tituna.