✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan ƙungiyar asiri da jarka guda ta jinin mutum a Zariya

Jinin wani mutum ne da suka yanka a yankin Barikin Jaji kuma mambobinsu sun tafi da sassan jikinsa zuwa Kaduna.

’Yan sanda sun sami nasarar kame wasu mutum bakwai ’yan wata ƙungiyar asiri mai suna Neo Black Movement yayin da suke ƙoƙarin ƙaddamar da sabbin mambobi a gundumar Dutsen Abba ta Karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.

Nasarar kamen ta biyo bayan bayan sirri da suka samu, inda aka kama cafke ababen zargin a harabar wata makabarta a yankin.

Waɗanda aka kama sun haɗa Samson Izikiel mai shekara 32, da Samuel Francis mai shekara 27 da kuma Usman Nura mai shekara 34.

Sauran sun haɗa da Gabriel Sheba mai shekara 23 da Haruna Said mai shekara 37 da Bala Lukuman mai shekara 27 da kuma Jabir Rilwan mai shekara 37.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an kama matasan bakwai ne a daidai lokacin da tsoffin mambobin ƙungiyar ke kokarin ƙaddamar da sabbin shiga.

A yayin gudanar da bincike, an same su da mota kirar Lexus Sedan da kuma bindigogi biyu ƙirar gida da kuma wata bindigar ƙirar Beretta da wukake da ƙwarya guda biyu da kuma jarka ɗaya cike da jinin mutum.

Bincike ya nuna cewa, jinin na wani mutum ne da suka yanka a yankin Barikin Jaji kuma sauran sassan jikin a cewarsu sauran ’yan ƙungiyar da ke zuwa daga Kaduna sun tafi da shi.

A halin yanzu dai dukkan waɗanda ake zargin suna ofishin ’yan sanda na shiyyar Zariya.

Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Masur Hassan ya tabbatar da lamarin da cewa suna ci gaba da binciken waɗanda ake zargin.