✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Raphael Varane ya yi ritaya daga taka leda

Varane ya yi shekara 10 a ƙungiyar Real Madrid, inda ya lashe kofi 18.

Tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid, Raphael Varane ya yi ritaya daga taka leda.

A watan Yuli ne Varane ya koma tamaula a ƙungiyar Como kyauta, amma ya ji rauni a wasansa na farko da suka fafata da Sampdoria a watan Agusta.

Sai dai ɗan wasan bayan mai shekara 31, ya ce zai ci gaba da kasancewa a ƙungiyar a wani matsayin daban ba na taka leda ba.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Varane ya ce “ba ƙaramin ƙarfin hali mutum yake buƙata ba wajen ɗaukar irin wannan matakin na sauroron jikinsa da zuciyarsa.

“Ina so ne na yi ritaya da mutuncina ba wai in ci gaba da tilasta jikina domin buga ƙwallo ba.

“Na sha faɗuwa sannan na tashi, amma a wannan karon, ina ganin ya kamata na haƙura da tamaula,” in ji shi.

“Sai dai ba na da-na-sani saboda babu abun da zan iya canjawa. Na samu nasarorin da ban taɓa zato zan samu ba.

“Sannan bayan nasarar lashe kofuna, ina alfaharin cewa duk runtsi duk wahala na kasance mutum mai gaskiya, sannan kuma duk inda na je, sai da na bar baya mai kyau. Ina fata na saka ku farin ciki da alfahari.”

A game da abin da zai fuskanta, Varane ya ce, “zan ci gaba da gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa amma ba a matsayin mai bugawa ba wanda zan bayyana a nan gaba kadan.”

Varane ya fara taka leda ne a ƙungiyar Lens ta Faransa, inda ya yi kaka ɗaya kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011.

Ya yi shekara 10 a ƙungiyar ta Spain, inda ya lashe kofi 18, ciki har da La Liga 3 da Kofin Zakarun Turai wato Champions Leagues huɗu.

Daga nan ne ɗan wasan ya koma Manchester United a farkon kakar 2021 a kan farashin farko na Fan miliyan 34, inda ya haska a wasa guda 95 a dukkan gasanni duk da fama da raunuka da ya yi.

Ya lashe kofin Carabao a Manchester United a shekarar 2022, sannan wasansa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne wasan ƙarshe na kofin ƙalubale wato FA, inda United ta doke Manchester City a watan Mayu.

A ƙasarsa ta Faransa, ya buga wasa 93, inda ya lashe Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2018 da Gasar Nations League a 2021, sannan yana cikin tawagar Faransa da suka sake kai wa wasan ƙarshe a Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2022.