11 ga watan Oktoba ita ce Ranar Yara Mata Ta Duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana don mayar da hankali kan bukatar magance kalubalen da ’yan matan ke fuskanta da kuma kara karfafa gwiwar ’ya’ya mata da biyan hakkokinsu.
Ganin cewa bana ake bikin karo na 10, da taken Yanzu Ne Lokacinmu: ’Yancinmu, Makomarmu, Aminiya za ta kawo muku rahotanni na musamman kan batutuwan da suka shafi ’ya’ya mata tun daga haihuwarsu zuwa zamansu manya.
- Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (2)
- Gwamnati na kashe $10m wajen ciyar da dalibai miliyan 10 —Ngige
Rahotannin sun shafi matsalolin da yara mata suke fusktanta, halin da suke shiga, mafita daga matsalolin da dai sauransu.
Misali, haihuwar yaro yawanci yana tare da wasu abubwa kuma kowace al’umma tana da irin naa al’adunta a wannan bangare.
Shin yaya abin yake a tsakanin al’ummar Hausawa? Haihuwar ’ya mace, alal misali, tana bukatar ayyuka da yawa da suka bambanta da na namiji.
Mene ne wadannan ayyuka, kuma ta yaya suke shafar makomar rayuwar yarinyar?
Ku kasance tare da mu.