Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, A’isha Isma’il, ta ce nagartar ilimin da ake bayarwa a makarantun gwamnati a Najeriya a zamaninsu daidai yake da wanda ake bai wa ’ya’yan turawa a kasar Birtaniya.
Ta ce a zamaninsu an fi daukar ’ya’ya mata da daraja kuma duk yarinyar da ta kammala makarantar sakandare, to tana da kwarewar da za ta iya gudanar da kowane irin aikin ofis a kowane mataki.
A hirarta da Aminiya albarkacin Ranar ’Ya’ya Mata ta Duniya ta 2022, Hajiya A’isha ta fayyace bambancin tarbiyyar ’ya mace da na da namiji da matsalolin kowannensu.
Ta kuma bayyana abin da ya lalata harkar ilimi a Najeriya da kuma hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar.