Kimanin allurar rigakafin cutar Coronavirus miliyan uku da dubu dari tara da ashirin nau’in AstraZeneca ce ake sa ran za ta karaso Najeriya ranar Talata.
Wannan ne dai zai kasance karo na farko da rigakafin za ta shigo kasar, lamarin da ya mayar da ita ta uku a Afirka ta Yamma da ta sami allurar bayan kasashen Ivory Coast da Ghana.
- Daga Jangebe ba za a sake sace dalibai a Najeriya ba – Buhari
- Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke gabansa a Kano
Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, Faisal Shuaib ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) suka fitar a Abuja ranar Lahadi.
Ya kuma ce adadin na daga cikin guda miliyan 16 da aka kudiri aniyar kawowa Najeriya a cikin rukuni-rukuni, a watanni masu zuwa.
Faisal ya kara da cewa, “Mun shirya sosai domin karbar wadannan alluran domin raba su ga ’yan Najeriyan da suka cancanta, a daidai lokacin da muka fara horar da ma’aikatan lafiya domin tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata a kowanne mataki.”