Daliban sakandare a Jihar Kano sun bukaci gwamnati ta inganta bangaren walwalar malaman makaranta domin samun karsashin koyarwa da ingantaccen ilimi.
Daliban sun bayyana hakan ne a ganawarsu da Aminiya, a bikin Ranar Malamai ta Duniya da Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta ware kowace ranar biyar 5 ga watan Oktoba domin ta.
- Shari’ar ASUU da Gwamnati: Kotun Daukaka kara za ta zauna kan hukuncin kotun ma’aikata
- NABTEB ta saki sakamakon jarrabawar NBC/NTC na 2022
Muhammad Mukhtar da ke karatunsa na Sakandare a Makarantar Tangaza da ke Kano, ya bayyana farin cikinsa da zuwan ranar, tare da rokon gwamnati ta duba bukatun malaman ta biya musu.
Ita ma wata daliba, Khadijah Nasir, ta ce malamai ne ruhin kowacce al’umma, don haka akwai bukatar kyautata wuraren da suke aiki, da kuma magance musu matsalolinsu.
Shi ma wani dalibi, Muhammad Bello, ya ce akwai bukatar girmama malamai duk inda suke.
“Akan samu wadanda ba sa girmama su, wasu kuma a yi dace idan sun girma su yi ta neman malaman nasu bisa mutuncin da suka yi musu lokacin da suke dalibai, domin su ma su kyautata musu,” in ji shi.
A karshe ya yi kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen inganta walwalar malaman, da biyan su hakkokinsu domin su ne ginshikin al’umma.