’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje
- Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas
Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki.
Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa da masu faɗan daban suka yi.
“Wasu sun fito faɗan daba, sun ji wa kansu raunuka a Ƙofar Na’isa, amma ba wanda ya zo wajen ’yan sanda a kai shi asibiti,” a cewar Kiyawa.
Sai dai Kiyawa ya ƙara da cewa jami’ansu sun sake komawa unguwar da daddare, inda suka cafke mutum takwas da raunuka a jikinsu da wuƙaƙe.
Kazalika, ya ce sun tattara sunayen mutane daban-daban da ake zarginsu da faɗace-faɗacen daba kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannu.
Aminiya ta rawaito yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin Ƙofar Na’isa da kuma Ƙofar Ɗan Agundi tun bayan dawowar faɗan daban a yayin bukukuwan sallah ƙarama da aka yi kwanan nan.