Gwamnatin Tarayya ta sanar da Litinin mai zuwa a matsayin ranar da za a dawo da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Yakub Mahmoud ne ya tabbatar da hakan ga wakilin Aminiya ranar Asabar.
- Ghana na shirin fara amfani da zinare wajen sayen mai a maimakon Dalar Amurka
- Ku ba Atiku shawara ya je gida ya huta ya hakura da takara – Tinubu
Ya ce gabanin dawo da sufurin a ranar ta Litinin, hukumar za ta fitar da cikakkun bayanai ga jama’a ranar Lahadi.
Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Ministan Sufurin Jiragen Kasa na Najeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ya sanar da cewa kafin karshen watan Nuwamban 2022 za a dawo da sufurin bayan shafe wata takwas da dakatar da shi.
Ministan dai ya ce za a dawo da sufurin ne kawai idan aka tabbatar da samar da isasshen tsaro a titunansa.
Ya ce dole a tabbatar da daukar wasu matakan tsaro kafin a kai ga dawo da sufurin, wanda ya hada da samar da na’urorin da za su rika sa’ido a kan kaiwa da komowar jirgin.
Sai dai wakilinmu bai iya tabbatar da ko kawo yanzu an kammala karkafa irin wadannan na’urorin a dukkan wuraren da ya kamata ba.
An dai dakatar da sufurin ne a watan Maris din da ya gabata, lokacin da ’yan ta’adda suka kai masa hari, inda suka kashe wasu fasinjojin suka kuma yi garkuwa da wasu.