✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Dimokuradiyya: Muhimman abubuwan da Buhari ya fada

Kada ’yan Najeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokuradiyya suka bayar a 1993.

A Najeriya a duk ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ake bikin zagayowar Ranar Dimukuradiyya.

An fara bikin wannan rana ce tun daga shekarar 2002, amma Shugaba Muhammadu Buhari ya kara mata karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya Ranar Dimokuradiyyar daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

A yayin jawabin da Shugaba Buhari ya gabatar a safiyar ranar Lahadi, ya soma ne da bayani kan muhimmancin Ranar, yana jaddada tasirin zaben Yunin 1993 a tarihin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce kada ’yan Najeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokuradiyya suka bayar a 1993.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su yi koyi da kishin kasa irin na magabata a duk lokacin da za su zabi shugabanni.

Shugaban ya sake tuna wa ’yan Najeriya cewa wannan ce Ranar Dimokuradiyya ta karshe da zai yi a matsayinsa na Shugaban Kasa inda ya ce yana cike da kudirin tabbatar da cewa an zabi sabon shugaban kasa ta hanyar zabe na gaskiya da adalci.

Haka kuma Shugaba Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani a kasar inda ya ce daya daga cikin abin da ya birge shi da zaben shi ne yadda mata da matasa a kusan duka jam’iyyun suka fito neman takara, “wannan alama ce da ke nuna dimokuradiyyar Najeriya ta kara bunkasa a cikin shekara 23 da aka shafe.

“Yayin da muke shiga kakar yakin neman zabe da kuma zabe na gama gari, kada mu taba daukansa a matsayin wani alamrari na a mutu ko a yi rai, dole ne mu tuna cewa dimokuradiyya ta yi tanadin abin da mafi rinjayen kaso na alumma suke so, saboda haka dole za a samu masu nasara da masu faduwa.

Shugaban ya bayyana cewa a shekara bakwai da ya shafe kan mulki, gwamnatinsa ta yi kokari wurin gyara Dokokin Zabe da yanayin gudanar da zaben domin kare kuri’un al’umma.

Kan dai batun zaben, Shugaba Buhari ya bayyana cewa bangaren Zartarwa da Dokoki da kuma Shari’a na da kudirin ganin sun aiwatar da wadannan sauye-sauye na Dokokin zabe a yayin zaben 2023.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci duk ’yan Najeriya su saka wadanda rikicin ta’addanci ya rutsa da su cikin addu’a, yana mai cewa a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya bayar da tabbacin cewa duk hukumomin tsaron kasar na yin duk mai yiwuwa domin ceto wadanda aka sace.

“Na san cewa muna cike da damuwa kan yadda ake fama da kalubale na matsalar tsaro a sakamakon ayyukan ta’addanci, a matsayinmu na gwamnati muna aiki tukuru don shawo kan wadannan kalubale.

“Don ganin an samu biyan wannan bukata, dole kowa ya bayar da gudunmawa. Ba aikin gwamnati ba ne ita kadai, akwai bukatar dukkan yan kasa su ba rika bai wa jamian tsaro hadin kai ta hanyar mika musu rahoton duk wani mutum da ake zargi da aikata laifi ko wani motsi da basu yarda da shi ba.

“Zan karkare wannan jawabi na Ranar Dimokuradiyya, wanda kuma shi na karshe da zan yi a matsayina na Shugaban kasa, ta hanyar tabbatar muku da kudirin da na dauka na kare Najeriya da ‘yan Najeriya daga dukkan makiya daga ciki da waje.”

Buhari ya rufe jawabinsa da cewa Allah Ya albarkaci Kasar Najeriya.