✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba.

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025.

A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba.

A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma.

Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya tun bayan ƙarewar mulkin soja a shekarar 1999.

A da ana yin bikin ranar dimokuraɗiyya a ranar 29 ga watan Mayu kowace shekara ranar da ake rantsar da shugabannin ƙasa da gwamnoni da ’yan majalisa.

Amma daga shekarar 2018, an sauya ranar zuwa ranar 12 ga watan Yuni domin tunawa da zaɓen 1993 da aka soke, wanda MKO Abiola ya lashe kuma da yawa na ganin wannan shi ne zaɓen da ya fi sahihanci a tarihin Najeriya.