Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Lahadi, 12 ga watan Yunin 2022.
Jawabin, wanda zai kasance na Bikin Ranar Dimokuradiyya ne za a watsa shi da misalin karfe bakwai na safe.
- ’Yan bindiga sun sako 11 daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 10 a Burkina Faso
Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Shehu ya bukaci dukkan kafafen watsa labaran gwamnati na rediyo da talabijin su yi aika kafada-da-kafada da tashoshin FRCN da NTA domin watsa jawabin kai tsaye.