✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Asabar za a kammala jigilar maniyyata Aikin Hajjin bana – NAHCON

Ta ce bana ba za a sami matsalar tsaikon jigilar ba

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce a ranar Asabar za ta kammala jigilar dukkan maniyyata Aikin Hajjin bana daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ce ta bayyana hakan na cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

A cewarta, “Nan da ’yan sa’o’i za a kammala jigilar maniyyata Aikin Hajjin bana.

“An shafe kwana 27 ana fafata jigilar kuma ya zuwa yanzu jirage 170 sun isa Jiddah da Madina inda aka kai maniyyata sama da 71,000, kuma ana ci gaba.

“Kafin yau, kamfanonin Aero Contractors da Max Air da Air Peace duka sun kammala jigilar maniyyatan da aka ba su, amma har yanzu Azman yana da ragowa.

“Kamfanin FlyNas, mallakin kasar Saudiyya ana sa ran zai kammala jigilar ta bana, sakamakon tsaikon da ya fuskanta tun farkon fara jigilar.

“A sakamakon haka, filin jirgin saman Jiddah zai ci gaba da zama a bude ga maniyyatan Najeriya su ci gaba da sauka har zuwa ranakun 23 da 24 ga watan Yuni,” in ji ta.

Fatima ta kuma ce jirgin da zai debi ragowar jami’an hukumar alhazai an shirya zai tashi ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni. (NAN)